Hare-haren 'yan bindiga ya dawo sabo wasu yankunan jihar Katsina

Hare-haren 'yan bindiga ya dawo sabo wasu yankunan jihar Katsina

Bayanai sun ce jama'ar garuruwa kimanin dari da hamsin na yankunan kananan hukumomin Malumfashi da Kankara na jihar Katsina, sun tsere zuwa wasu wurare.

Jama'ar da abin ya shafa sun koka da cewa, 'yan bindigan suna cin karensu ba babbaka, saboda rashin kwararan matakan tsaro.

Matsalar hare-haren 'yanbindiga da ta zama wani karfen kafa a yankin arewa maso yammacin Najeriya tana ci gaba da jefa jama’a a cikin tsaka mai wuya a garuruwa da dama na karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

''Yanzu halin da ake ciki abubuwa sun dawo fiye da da, zuwa an jima sai ka ji abin da ya faru, ko sun kashe wani ko sun dauki wani ko kuma sun kora shanun wani'' in ji shi.

Mazaunin yankin ya yi ikirarin cewa matsalar ta sa mazauna garuruwa 20 tserewa daga gidajensu kuma a cewarsa ‘duk sun koma tamkar kufai’:

‘’Su barayin da sun shigo ko su kona garin, daki-daki wasu kuma da suka fito ana harbinsu. Wannan shi ne ya sa asarar rayukan ta yi yawa kuma ‘yan bindigar suna kashe jama’a fiye da kima kuma sai su kwashi sama da awa uku suna cin karensu ba bu babbaka ka ga babu jami’in tsaron da zai zo in ji shi''.

A yankin karamar hukumar Kankara ma, matsalar ta 'yan bindiga ta dawo sabuwa a wasu wuraren, har ta fasa garuruwa fiye da dari a kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC.

‘’Kana zaune gidanka a zo a kore ka, a harbe ka, dole kana ji kana gani ka bar yayanka, ka bar matanka ka ruga da gudu, in kuma ba ka samu sa’a ba a zo a banke ka da mashin'' in ji shi.

Ya kuma ce akwai rashin tabass game da makomar yankunan saboda ko a baya-bayan nan sun yi kokarin komawa gidajensu amma sun sake haduwa da ‘yan bindigar.

‘’Mun je kwasar kayanmu sai ga mutanen nan sun zo mana, mai yar waya aka kwace, wasu kuma aka harbesu. Cikin dare kuma sun biyo suna kone mana gidaje, amfanin gona wanda muka baro na abinci sun kone. An kuma sace mutane wadanda ban san adadinsu ba,’’ in ji shi.

Ya kuma suna cikin halin haulahi a wuraren da suka yi gudun hijira

‘’Wallahi muna cikin hali na ha’ula’i saboda rijiyoyin da ake dibar ruwa ma janyewa suke ta yi saboda yawan jama'a’’ in ji shi.

BBC ta yi kokarin jin ta bakin rundunar 'yansandan Najeriya da kwamishinan tsaro na jihar game da wannan al'amari amma kuma hakar ba ta cimma ruwa ba saboda mun kasa samunsu ta waya har ya zuwa lokacin kammala wannan rahoto.