Tafiyar Gwamnatin Ahmad Aliyu ta saɓawa muradun Talakkan Sakkwato---Sani Yakubu

Tafiyar Gwamnatin Ahmad Aliyu ta saɓawa muradun Talakkan Sakkwato---Sani Yakubu
 
 
Honarabul Sani Yakubu dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gudu da Tangaza a majalisar wakillai ta Tarayyar Nijeriya ya kalubalanci yadda gwamnatin jihar Sakkwato ke tafiyar da jagorancinta don ta sabawa muaradun talakan jihar, tana yi gaban kanta a shiraruwan da take yi.
Dan majalisar a wani taro da ya kira don ganawa da mutanen da yake wakilta a satin da ya gabata ya ce "ku zo mu hadu da ku, domin cika alkawalin da aka dauka.
In yau za a ce an dauki wani dan uwan Gwamna[Garkuwa da shi) za a dauki mataki, tau mi  ya sa ku za a dauki 'yan uwanku a tsaya haka tau mi ya yi, ni sai na fadi gaskiya," a cewar Sani Yakubu
Ya cigaba da cewa ku dubi abin da ake yi Sakkwato a sanya waya a kowace unguwa har zuwa filin jirgi, ina amfaninta ga wanda ke jin yunwa da wanda ke rike a hannun 'yan ta'adda ana yi masa ruwan sama  a daji, don mi za ka yabi gwamnati da abin da ba a yi ba.
"Matukar za ku cigaba da yabon gwamnati tau kuna cikin walakanci an hana maku noma, amma sai a kawo maku buhun shinkafa daya ku rika tabi, bayan ka san da an barka ka yi noma kai ne za ka ba da buhun sadaka, akwai haushi anan a baka abin da ba zai wuce ya yi maka sati daya ba ya kare, sabanin ka noma abinka sai ya yi maka wata uku kana amfani da shi, yakamata muatane su dawo cikin hayacinsu.
"In gwamnati ba ta bayar da babura ga 'yan sintirin mu ba ni zan ba su, akwai haushi sama da wata bakwai an sawo babura an nunawa duniya za a rabawa jami'an tsaron jiha amma an mayar da su gidan gwamnati, gwamnatin nan ta shekara daya duk abin da tace za ta raba ba ta bayar ba sai dai kokarin a yi hoto a mayar a aje",kalaman Sani Yakubu wanda yake dan jam'iyar APC  ne.