Abin Da Ya Sa Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Tambuwal a Matsayin Sanatan Sokoto Ta Kudu 

Abin Da Ya Sa Kotu Ta Tabbatar da Nasarar Tambuwal a Matsayin Sanatan Sokoto Ta Kudu 


Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta jihar Sakkwato ta tabbatar da nasarar tsohon gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal a zaɓen Sanatoci na 2023. 

Kotun zaɓe ta tabbatar da Tambuwal a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Sanata jihar Sakkwato ta kudu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.
Tun da farko, ɗan takarar jam'iyyar APC, Abdullahi Danbaba, ya kai ƙara gaban Kotun inda ya kalubalanci nasarar Aminu Tambuwal na PDP, Channels tv ta ruwaito.
Ɗanbaba ya roƙi Kotun da ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda rashin bin ka'idojin dokar zabe.
Ya kuma bukaci kotun da ta bayar da umarnin sake zabe a rumfunan zabe 28 waɗanda yake zargin ba a gudanar da zaben ba a zaɓe watan Fabrairu da ƙarishen da aka yi a watan Afrilu. 
Da take yanke hukunci, Kotun ta yi watsi da karar saboda rashin cancanta, tana mai cewa takardun shaidun da mai ƙara ya gabatar ba su da inganci. 
Kotun ta kuma umarci mai ƙara ya biya waɗan da ake tuhuma na ɗaya daga biyu Naira N200,000 kowanensu watau Sanata Tambuwal da kuma jam'iyyar PDP. 
Tambuwal, tsohon gwamnan jihar Sokoto wanda ya shafe zango biyu a kan mulki, ya lashe zaben Sanatan Sokoto ta kudu da kuri’u 100,860.