APC Ta Rasa Kujerar Majalisar Tarayya Ga PDP a Sokoto 

APC Ta Rasa Kujerar Majalisar Tarayya Ga PDP a Sokoto 
Kotun daukaka kara dake birnin Tarayyar Abuja a ranar  litinin ta tsige Hon. Sa'adu Nabunkari daga kujerarsa ta dan majalisar wakilai Mai wakiltar kananan hukumomin Binji/Silame ta tabbatar dana jam'iyyar adawa ta PDP Hon. Mani Maishinko Katami.
Kotun daukaka karar ta sallami Nabunkari Binji daga kujerarsa ne bisa wata kara da abokin hamayyarsa ya saka na tuhuma akan rashin sahihancin takardun karatun sa wanda kuma kotun ta tabbatar.
Tun daga farin dai Alhaji Mani Maishinko Katami da jam'iyyarsa ta PDP sun garzaya karamar kotun dake Sokoto suna Kalubalantar Nasarar Sa'aadu Binji daga bisani kotun ta kori karar, anan suka daukaka karar wadda kotun ta bashi Nasara a jiya litinin.
Wannan hukumcin na zuwa ne Daidai lokacin da wata kotun daukaka karar dake Abuja tayi watsi da karar dan takarar Gwamnan Sokoto na PDP Sa'idu Umar Ubandoma wadda yake Kalubalantar Nasarar gwamna Ahmad Aliyu.
Jami'in Hulda da jama'a a jam'iyar PDP Hassan Sahabi Sanyinnawal ya tabbatarwa Managarciya an gudanar da hukuncin a Abuja, bayan yanke hukuncin sun taya Wanda ya samu nasara murna domin cigaba ne jam'iyarsu ta samu.