Yan Bindida Sun rufe hanayar Funtuwa Zuwa Gusau, Sun yi Garkuwa da matafiya da dama

Yan Bindida Sun rufe hanayar Funtuwa Zuwa Gusau, Sun yi Garkuwa da matafiya da dama

'Yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani direban Tirela sun yi garkuwa da mutane matafiya da dama daki cikin wasu motoci uku a babbar hanyar Funtuwa zuwa Gusau.
'Yan bindigar sun rufe hanyar ne sama da minti 30 suna harbi ta ko'ina kan mai uwa da wabi. 
A cewar wanda ya gani abin da ya faru ya ce lamarin ya faru ne kusa ga garin Magazu kusa ga karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Sojoji sun kawo dauki bayan an yi ta kiran su a waya, sun zo da motoci hudu masu dauke da bindiga in da suka kora 'yan bindigar cikin daji, abin da ya sa masu motoci suka samu hanyar wucewa.
Wani mai mota da ya tsalke rijiya da baya ya ce 'yan bindigar suna da yawan gaske.
Har zuwa hada rahoton 'yan sanda a hukumance ba su ce komai kan lamarin ba.