Daya daga cikin Jigogin jam'iyar PDP a jihar Sakkwato Honarabul Buhari Sidi Attahiru ya yi magana kan Sanata Ibrahim Lamido da yadda yake ganin cancantarsa na abi shi a gidan siyasa da wakilicinsa ga wadanda suka zabe shi a gabascin jiha.
Honarabul Buhari yana da yakinin wannan tafiyar ta Sanata Lamido za ta haifar da cigaba a jihar Sakkwato kamar yadda ya soma a wakilcin da yake yi wa Gabascin Sakkwato.
"Hanyar Sanata tana bullewa kasan akwai bambanci tsakanin mai nema wurin wani da mai nema ga Allah, shi Lamido na kokarin yin abin da ya yiwa al'umma alkawali, saboda hakan Allah zai ba shi nasara, ai an taba samun irin haka a baya a nan Sakkwato lokacin da Sanata Wamakko ya zama gwamna bai tare da Gwamna a lokacin, kuma dukan jagorori a lokacin ko daya basa goyon bayansa, amma Allah ya ba shi mulki.
"Karfin da Lamido ya shigo da shi a siyasa a lokacin da Wamakko ya shigo bai da irin wannan karfin, kuma Allah bai hana shi ba, abin da ke gaban mutum ya yi abin da ya dace sauran lamari ka barwa Allah, bana ganin sun isa su hana shi cin nasara abin da zai yi don suna da mulki, ana iya kayar da gwamna a lokacin da yake saman kujera, yanzu ba lokacin kamfe ba ne amma ko ta Shugaban kasa Lamido ya nema muna yi masa fatar alheri da rokon Allah ya tabbatar da shi kanta don ya cigaba da yin aiyukkan alheri da yake yiwa jama'a." a cewar Honarabul Buhari.
Ya kara da cewar a halin da ake ciki yanzu da yanda al’umma da kasa suke ciki yakamata, "mu fuskanci abin da yake gaskiya a kowace jam’iya mutum ya fito ko ba a jam’iyar da kake goyon baya ba ne, tau ka ba shi goyon baya, ni a jam’iyar PDP na fito a ciknta nake kuma a cikinta aka sanni mafiyawan mutanen da suka sanni a siyasa a cikinta ne amma a halin da ake ciki ba wai ina goyon bayan jam'iyar APC ba, da ake ta yawo da maganar a wasu kafafen yada labarai a jiha, ina bayar da goyon baya ne ga wani mutum dan jam'iyar APC dana fahimta yanada nagarta da kokarin cika alkawalin da ya dauko wa al'umma, mafiyawa muna da matsalolin 'yan siyasa wanda in aka zabe su kuma shikenan in sun samu mulki za su tafiyarsu amma sai ga wani mutum mun gani a wata jam'iya yana kokari yana yin har abin da bai yi alkawali ba wannan yana cikin abin da ya ja ra'ayina na fito a fili, na bayyanawa duniya goyon bayana ga Sanata Ibrahim Lamido wanda yake wakiltar Sakkwato ta Gabas ka ji yanda lamarin yake."
Honarabul ya yi magana kan gwamnatin Sakkwato ya ce "Gwamnatin Sakkwato ta kasa, a tawa fahimtata domin naji gwamnan Sakkwato na fadin in duk allocation na Sakkwato zai kare sai ya samar da tsaro, wannan abin a bayane yake ba a yi ba kuma ba a dauko hanyar yi ba, matakin da aka dauka ban gamsu da shi ba, maganar ba zai bari a ci kudin jama'a ba shi ma bai yi ba, alkawarin da aka yi cikin kashi 100 ba a yi biyar ba, kamar mulkin yafi karfinsu ne, suna tunka da walwala sun kasa fa a tunanina, ba su kula hakkin al'umma, jama'a sun yi daban gwamnati ta yi daban akwai alamar rashin kwarewa da son rai, in kana fitowa kana sukar su za a yi amfani da gurbatattun jami'an tsaro a kama ka a ci ma zarafi, kamar matashin da aka kai gidan yari kan bidiyon matar gwamna ga kuma matashiya Hamdiyya don ta fadi abin da take da dama a doka ka ga abin da aka yi mata," kalaman Buhari Sidi.