Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe.
Wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki a jihar Yobe, daga qananan hukumomin Bade da Jakusko sun gudanar da gangamin nuna rashin jindadi tare da sake yin kira ga uwar jam'iyyar ta qasa da cewa ta yi musu adalci wajen zaven fidda-gwani a mazabar Bade/Jakusko a kujerar majalisar wakilai, sun bayyana rashin gudanar da sahihin zaben tamkar tauye hakkin al'ummar yankin ne a dimukuradiyance.
Wadannan kiraye-kirayen sun fito ne daga bakin dan takarar kujerar majalisar wakilai, mai wakiltar Bade/Jakusko, Hon. Sani Ahmed Kaitafi tare da magoya bayan sa a wani gangamin da su suka shirya ranar Litinin a garin Gashuwa, hidikwatar karamar hukumar Bade dake jihar Yobe, inda suka nanata yin kira da bukata ga uwar jam'iyyar cewa, kimanin kwanaki biyar da suka gabata wanda jam'iyyar APC ta fara gudanar da zaben fidda-gwani a fadin Nijeriya, yayin da har yanzu ba a gudanar da na Bade/Jakusko ba.
Magoya bayan dan takarar sun dora zargin kin yin zaben ne ga kwamitin da uwar jam'iyyar ta tura a yankin, wanda hakan ya saba wa tanadi da kudurin jam'iyyar APC wanda ya kunshi yi wa kowane dan jam'iyya adalci ta hanyar gudanar da shi ko kuma sulhu tsakanin yan takara domin samun hadin kai da ci gaban jam'iyyar da al'umma baki daya, inda suka kafe kan cewa, "amma babban abin mamaki, ko daya bai yuwu ba; ba a yi zaben fidda-gwani ba balle kuma sulhunta yan takarar."
"Yau kwana biyar cur (Jummu'a zuwa Litinin) da fara gudanar da zaben, amma abin takaici an ki gudanar da na Bade/Jakusko, alhalin takwarorin yankin a jihar Yobe da sauran yankunan Nijeriya sun yi nasu, kuma har yanzun nan ba a gaya mana dalili ba. Sai kawai mu ka ji labari a sama cewa wai wani ya ci zaben. Abin tambaya shi ne; a ina aka gudanar da zaben kuma a gaban wa aka yi shi? Saboda mu dai iya sanin mu ba a gayyaci dan takarar mu ba kuma ba a yi zaben ba inda uwar jam'iyyar APC ta ayyana."
A wannan gangamin wanda magoya bayan Hon. Kaitafi su ka gudanar, sun yi kira ga uwar jam'iyyar APC ta qasa ta shiga lamarin tare da yi musu adalci wajen gudanar da zaben fidda-gwani a mazavar Bade/Jakusko da ke jihar Yobe, kamar yadda ta yi a sauran yankunan jihar da a kowace mazava a fadin qasar nan.
Daruruwan magoya bayan wadanda suka gudanar da taron gangamin a wasu titunan garin Gashuwa, kana kuma dauke da kwalaye da alluna an rubuta mabanbantan bayanai wadanda suke dora zargi ga kwamitin da jam'iyyar APC ta dorawa alhakin zaben fidda-gwanin, bisa yadda suka ki gudanar dashi face kawai sun shiga daki tare da rubuta sunan wani mutum wanda ba shi ne zabin al'ummar yankin ba.
Da yake jawabi ga dandazon matasan da suka gudanar da gangamin, Daraktan yaqin neman zaven Hon. Kaitafi, Mallam Bukar Dala ya bayyana cewa, "Bamu gamsu ba, saboda sam ba a gudanar da zaben fidda-gwani ba, kawai sai labarin muka ji cewa sun shiga daki tare da rubuta sunan wani mutum a matsayin wanda aka zava alhalin babu inda aka yi zaben- wannan wasa da hankali ne kawai suka yi." In ji shi.
Shima Malam Bashir Rankas ya yi qarin hasken cewa, "Bisa gaskiyar zance shi ne; duk da na matsayinmu ya'yan jam'iyyar APC, amma ba a gudanar da zaben fidda-gwani na mazavar Bade/ Jakusko ba, kuma mun yi mamakin yadda hakan ya faru saboda mun ga yadda aka gudanar dashi a faxin qasar nan. Saboda haka muna kira ga uwar jam'iyyar APC ta qasa ta yi wa al'ummar wannan yanki adalci a zo domin gudanar da shi tare da bai wa jama'a dama su zabi dan takarar da suke so. Sannan mu na so manyan mu su gane dangane da irin abin da muke qoqarin kaucewa faruwar sa, don gaskiya jama'a sun harzuqa matuqa." In ji shi.
A nashi vangaren, Hon. Sani Ahmed Kaitafi, dan takarar kujerar majalisar wakilai a mazabar Bade/Jakusko, ya yi kira ga magoya bayan sa cewa kowa ya kwantar da hankalin shi, sannan ya buqaci uwar jam'iyyar APC ta duba lamarin tare da yi wa al'ummar yankin adalci.
Ya ce, "Ta la'akari da yanayin da ake fuskanta na tunkarar babban zabe a Nijeriya na 2023, wanda wasu jam'iyyu kan karkata zuwa ga yan takarar da wasu jam'iyyu ke qoqarin take musu haqqi, wanda hakan kan iya kai wasu zuwa ga canja ra'ayi wajen canja sheqa ko kuma su rungumi kaddara." Ya bayyana.