Ubandoma Yafi Kowane Dan Takara Cancanta Don Ba Wani Aibu Da Za Ka Fadi Kansa----Abdullahi Hassan

Ubandoma Yafi Kowane Dan Takara Cancanta Don Ba Wani Aibu Da Za Ka Fadi Kansa----Abdullahi Hassan

 

Tsohon shugaban karamar hukumar Sakkwato ta Arewa jigo a jam'iyar PDP a jihar Sakkwato Honarabul Abdullahi Hassan ya yabi dan takarar gwamnan Sakkwato a jam'iyar PDP Alhaji Sa'idu Umar Malam Ubandoma tare da ganin yafi kowa cancanta a cikin masu takara da shi don ba a san aibinsa ba.

 
"Magana ta hakikani, duk dan takarar da muke da shi a Jiha(Sokoto) kaf, ban cire maka kowa ba, ban da wanda nake  ganin ya cancanta kamar shi a shari'ance," a cewar Abdullahi Hassan. 
 
Ya ce "Mutum ne Mai Ilimi na Addinin Musulunci, mutum ne mai ilimin Boko, mutum ne mai tawadu'i, ba ka ganin shi kaga wata fahariya a tare da shi, mutum ne wanda gwargwado an shede shi da mutunci, mutuntawa da kuma karrama mutane.
 

"Kuma idan ka duba duk wanda ya fito takara, sai ance wani abu  akan shi, to Alhamdulillah babu wani abu na aibi, wanda wani zai iya fitowa ya fadi kan Malam Sa'idu Umar (Ubandoma), a cewar Mai Malale.