Tinubu, Gowon, Osinbajo Sun Halarci Kaddamar da Littafin Karrama Buhari
Shugaba Bola Tinubu, tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), na daga cikin manyan baki da suka halarci bikin kaddamar da wani littafi mai suna 'Aiki tare da Buhari: Reflections of a Special Adviser Media and Publicity, 2015-2023' a ranar Talata.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari; tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, uwargidan tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari, da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Littafin wanda tsohon mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina ya rubuta, an gabatar da shi ne tare da mujalladi biyar na wani littafi mai suna 'Muhammadu Buhari, The Nigerian Legacy, 2015 to 2023'.
Taron kaddamar da littafin wanda aka gudanar a dakin taro na Congress Hall of Transcorp Hilton Hotel dake Abuja, ya kasance ziyarar aiki ta farko da Buhari ya kai babban birnin tarayya tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da ya mika wa Tinubu.
Taron kuma shi ne karo na farko da Tinubu da Buhari za su bayyana tare a bainar jama'a tun bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
Credit: Channels TV
managarciya