'Yan Bindiga Sun Kai Mummunar Hari a Zamfara, Mutum 4 Sun Mutu Yayin da Aka Sace 150

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunar Hari a Zamfara, Mutum 4 Sun Mutu Yayin da Aka Sace 150

 

'Yan bindiga sun halaka mutane hudu tare da yin garkuwa da wasu mutum 150, ciki har da jarirai 'yan watanni shida da takwas.

Wannan ya faru ne a farmakin da miyagun suka kai kauyen Dan Isa dake karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara a ranar Lahadi. 
Dan Isa na nan a kusa da Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Kauyen yana da nisan kilomita 14 daga babban birnin, Daily Trust ta bayyana haka. 
Wannan farmakin na zuwa ne mako daya bayan da 'yan bindiga suka sako mazauna yankin Dogon Kade 46 bayan an biya kudin fansa da ya kai Naira miliyan 21. 
Wani mazaunin Dan Isa, wanda aka sace matarsa da dansa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai. 
Mazaunin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce 'yan bindigan sun tsinkayi kauyen wurin karfe 3 na tsakar ranar Lahadi kuma sun kwashi awanni shida suna barna. 
"Matata, Na'imah da jaririnmu Sudai mai watanni shida suna daga cikin wadanda aka sace. Matar dan uwana, Aisha da jaririnta mai watanni takwas duk an sace su." 
Wani mazaunin yankin, Muhammad Auwal, ya ce Hajiya Rakiya, matar Wamban Dan Isa, Alhaji Bello Halilu, na daga cikin matan da aka sace kuma an raunata wasu a gidan Halilu. 
Matan kanin Wamban Dan Isa, Malama Luba da Malama Talatu suna cikin wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda Malam Auwal ya bayyana. 
Malam Auwal ya ce: "Na gano cewa Malam Musa Ajiya yana daga cikn wadanda suka arce daga hannun 'yan bindigan amma mata hudu har da matarsa da matar kaninsa an tafi da su. 
Aminu Bello Dan Isa, wani mazaunin yankin, ya ce kungiyar ta'addancin karkashin jagorancin Alhaji Shehu Bagiwa ne suka kai farmakin. 
Duk da majiyoyi sun tabbatar cewa babu Bagiwa cikin harin kai tsaye, matan da suka tsere sun ga babban yaronsa, Aminu Baka-da-dadi, yana jagorantar harin.