Tsohon Sakataren kudin jam’iyyar ACN ya fito neman shugabancin jam'iyyar APCn jihar Tarab
Alhaji Muhammad Dan Atiku Jalingo,wanda ya taba zama babban sakaraen jam’iyyar Action Alliance AC kafin ta koma ACN wanda kuma tsohon dan takarar gwamna ne a karkashin inuwar jam’iyyar NCP (National Conscience Party) a jihar Taraba a shekara ta 2003 yanzu ya fito neman shugabancin jam’iyyar APC na jihar Taraba
Tsohon Sakataren kudin jam’iyyar ACN ya fito neman shugabancin jam'iyyar APCn jihar Taraba
Daga Habu Rabeel, Gombe
Alhaji Muhammad Dan Atiku Jalingo,wanda ya taba zama babban sakaraen jam’iyyar Action Alliance AC kafin ta koma ACN wanda kuma tsohon dan takarar gwamna ne a karkashin inuwar jam’iyyar NCP (National Conscience Party) a jihar Taraba a shekara ta 2003 yanzu ya fito neman shugabancin jam’iyyar APC na jihar Taraba
Dan Atiku yace yana son ce to jam’iyyar ta su ce da jihar Taraba daga halin da suke ciki shi yasa yake neman zaman shugaban jam’iyyar saboda kwarewar da yake da shin a shugabanci
A cewar sa ida ya zama shugaban jam’iyya zai yi kokari ya ga sun sake kafa gwamnati a shekarar 2023 sun kori jam’iyyar PDP a fadin jihar Taraba.
Baya ga zaman sa Sakatare a ACN Dan Atiku ya rike mukamai daban daban ciki har da Sakataren gunduma na jam’iyyar social Democratic party SDP a shekarar 1989 kana daga bisani ya zama PRO a shekarar 1993 sannan kuma a 2002 ya zama shugaban jam’iyyar NCP a 2003 ya yi mata takarar gwamna a jihar ta Taraba
Muhammad Dan Atiku Jalingo, ya yi amfani da wannan damar wajen neman hadin kai da goyon bayan al’ummar jihar Taraba musamman wadanda suke da kuri’a da su zabe shi dan ya zama shugaban jam’iyyar a zaben da za’a gudanar a ranar 2 ga watan Oktoba na wannan shekarar
managarciya