@world Press Freedom Day: Manema Labarai A Nijeriya Na Cikin Mawuyacin Hali
@world Press Freedom Day: Manema Labarai A Nijeriya Na Cikin Mawuyacin Hali
Manema labarai a Nijeriya sun bayyana irin mawuyacin halin da suke ciki a lokacin da suka marawa takwarorinsu na duniya kan ranar 'yan jarida ta duniya ta wannan shekara.
Sun bayyana damuwarsu kan damar bayyana ra'ayi da ƙasar ta tauye, musamman al'amurran cin zarafi, kamawa da tsarewa da suke fuskanta.
Shugaban 'yan jarida na ƙasa Chris Isiguzo a lokacin da yake magana da Daily Trust ya bayyana damuwarsa kan ƙalubalen da 'yan jarida ke fuskanta a cikin yanayin sadarwar zamani.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gormama tare da ba da damar bayyana albarkacin baki kamar yadda doka ta tanada.
Ya ce yaɗa labarai su ne iskan shaƙa na dimukuraɗiyya, su ne ke sa ta yi tasiri.
managarciya