Buɗe Kasuwar Zamani: Sanata Lawan Ya Baiwa 'Yan Kasuwa Tallafin Miliyan 200 a Yobe

Buɗe Kasuwar Zamani: Sanata Lawan Ya Baiwa 'Yan Kasuwa Tallafin Miliyan 200 a Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Gwamnan jihar Yobe Hon. Mai Mala Buni tare da Sanata Lawan sun kaddamar da bude sabuwar kasuwar zamani (Ultra-Modern Market) wadda gwamnatin sa ta gina a garin Gashuwa, tare da sanya wa kasuwar sunan Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ranar Assabar. 

Da yake jawabin maraba a lokacin bude kasuwar, Kwamishinan Ma’aikatar Kasuwanci a jihar Yobe, Alhaji Barma Shettima ya bayyana sabon aikin kasuwar a matsayin ma’auni kuma mafi ingancin aikin wanda ya dace da tsarin zamani da samar da yanayi mai kyau a harkokin kasuwanci.

A jawabin sa na godiya shugaban kungiyar yan kasuwar karamar hukumar Bade, Alhaji Babangida Sabo, ya yaba wa gwamnatin jihar Yobe a karkashin Gwamna Mai Mala Buni kan aikin gina kasuwar wanda ya ce zai taimaka matuka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin da jihar Yobe baki daya.

A jawabin Gwamna Buni sa'ilin da yake kaddamar da sabuwar kasuwar, ya bayyana sanya wa kasuwar sunan Sanata Ahmad Ibrahim Lawan.

Ya kara da cewa, “Sanata Lawan shi ne Shugaban Majalisar Dattawa na farko daga jihar Yobe, daga yankin Arewa maso Gabas, wanda bisa la’akari da gudunmawar da ya bayar don ci gaban wannan jihar, kana da kyakkyawan alakar da yake da ita da gwamnatin jihar Yobe; abin a yaba ne tare da jinjina masa.”

Ya ce, “Wannan sabuwar kasuwar zamani da muka gina a Gashuwa, ta kunshi shaguna 505, ofisoshin gudanarwa, masallaci, magudanan ruwa, ofishin kashe gobara, da ofishin yan-sanda da makamantan su." In ji Gwamna Buni.

"Mun gina kasuwar ne domin habaka Harkokin tattalin arziki wanda zai samar da guraben ayyukan yi, samar da kudin shiga ga jama'armu da kuma inganta kudaden shiga da ake samu a cikin gida."

Gwamna Buni ya kara da cewa, domin samun saukin gudanarwa, gwamnatin jihar ta yi wa kasuwar rajista a matsayin kamfani tare da kafa kwamitin da zai sanya ido wajen gudanar da ita. Inda ya umarci kwamitin gudanar da kasuwar ya yi aiki don tabbatar da an cimma manufa.

A nashi bangaren, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, a karkashin gidauniyarsa ta SAIL, ya bai wa yan kananan yan kasuwar tallafin Naira miliyan 200 domin habaka jarin kasuwancin su.

Bugu da kari kuma, Sanata Lawan ya ce kimanin yan kasuwa 400 ne za su ci gajiyar tallafin Naira 500,000 kowane mutum daya a matsayin jarin fara sana'a. 

Haka kuma ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Yobe wajen gina kasuwannin samani guda biyu a yankinsa a Gashuwa da Nguru.

“Saboda haka a madadin al'ummar Arewacin jihar Yobe, ina mika godiyarmu dangane da wannan kulawa da muka samu daga gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni ta hanayar aiwatar mana da manyan ayyukan ci gaba." In ji Sanata Lawan.