Sanarwa Kan Wani Cigaba Da Managarciya Ke Son Fitowa Da Shi

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Amadadin hukumar gudanarwa ta MANAGARCIYA, muna sanar da masu bibiyar shafukan mu cewa mun shirya tsaf domin fadada bayar da labaranmu a cikin harshen Turanci daga sati mai zuwa.
Muna son ku fahimce mu da cewa wannan kafar bayar da labarai ta gano akwai masu bibiyarta da ba su iya karatun Hausa kuma suna da sha’awar bibiyar shafukanta, domin tafiya da kowa muka fitar da bangarori uku da za mu rika rubutu a cikinsu da harshen Ingilishi, wanda suka hada da News, Health, Insurance.
Labaranmu da muke bayarwa a sauran bangarori cikin harshen Hausa ba a abin da ya taba su, kawai wannan wani cigaba ne da ake ganin yakamata a samar a wannan kafar.
Masu bibiyar mu muna neman shawararku kan wannan tsarin da muka fito da shi.
Don aika mana shawara a tuntube mu a managarciya@gmail.com ko 09019442973(wasup).
Edita Managarciya.