Mutum 14 Sun Mutu a Haɗarin Mota a Jigawa

Mutum 14 Sun Mutu a Haɗarin Mota a Jigawa

Haɗarin mota ya rutsa da wasu mutane 14 a babbar hanyar Kanya, in da aka kwantar da mutum 4 asibiti.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata in da Tirela ta yi taho mu gama da mota hiace in da shedun gani da ido ya ce karamar motar ne tafe da gudu tana son ta wuce babbar mota.
Lamarin ya yi sanadin rasa rayukan mutane 14 aka kai 4 asibiti, likita ya tabbatar da mutuwar a asibitin Cottage.