Gwamnatin Gombe ta biya Diyyar Mutanen Billiri da rikici ya rutsa da su 

Gwamnatin Gombe ta biya Diyyar Mutanen Billiri da rikici ya rutsa da su 

 

 Daga: Abdul Ɗan Arewa

 

Gwamnatin jihar Gombe a ranar Litinin ta biya N591m a matsayin diyya ga wasu waɗanda rikicin rikicin ya rutsa da su a karamar hukumar Billiri a watan Fabrairu kan rikicin Sarauta ta Mai Tangle.

 

Kimanin mutane 554 da abin ya shafa wasu sun amfana da N40m a Fadar Mai Tangale dake Billiri, wurin taron.

 
Ku tuna cewa an jefa Billiri cikin tashin hankali sakamakon bullar sabon Mai a masarautar Tangle bayan rasuwar Mai Tangle na 15, Abdul Buba Maisheru.
 
Musabbabi  zanga -zangar ya faru ne saboda rahotannin dake cewa gwamnatin jihar za ta ayyana babban Mai Tangle a kan dan takarar da ya fi kowa yawan kuri'u.
 
Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta dogara da dokar jihar dake da ita wacce ta ba ta 'yancin yin watsi da shawarar masu yin sarauta a irin wannan hali.
 
Kwamishinan kuɗi, Muhammad Magaji, wanda ya zanta da waɗanda suka amfana, ya yi bayanin cewa za a raba kuɗin a tsakanin ƙungiyoyi biyu da suka hada da iyalai takwas da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka yi asarar dukiya a rikicin.
Wannn wani abin yabawa ne a karamin lokaci gwamnati ta cika alkawalin da ta dauka kan wadanda rikici ya afkawa a yankin.