NCC ta amince da karin kashi 50% na farashin data da na kiran waya

NCC ta amince da karin kashi 50% na farashin data da na kiran waya

Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta amince da karin kaso 50% a farashin kiran waya da data  na kamfanonin sadarwa, tana mai bayyana dalilai na karuwar kudaden gudanarwa da kuma bukatar ci gaba da kula da harkar sadarwa a kasar.

An sanar da wannan amincewa ne a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, inda aka bayyana cewa wannan karin ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da karin sama da kaso 100% da wasu kamfanonin sadarwa suka nema.

A cewar NCC, wannan gyaran farashi ya yi daidai da huruminta karkashin Sashe na 108 na Dokar Sadarwa ta Najeriya ta shekarar 2003, wadda ta ba da izini kan kula da farashin .