Dan majalisa ya nemi Gwamnatin Sokoto ta dawo da wutar lantarki a wasu kauyukkan jiha

Dan majalisa ya nemi Gwamnatin Sokoto ta dawo da wutar lantarki a wasu kauyukkan jiha
 

 

Alhaji Abdullahi Muhammad Randa Dan majalisa Mai wakiltar karamar hukumar Tureta a majalisar dokokin jiha ya bayyana damuwarsa yanda karamar kankarar ruwan sanyi ta yi tsada sosai in da ake sayar da duk daya naira 1000 a wasu wurare na yankinsa cikin Watan Ramadan.

Alhaji Randa Dan jam'iyar PDP ne ya gabatar da kudiri gaban majalisa na gaggauta kira ga gwamnatin jiha ta yi maganin matsalar wutar lantarki da ke addabar yankinsa.
Alhaji Faruku Sidi Dan jam'iyar APC dake wakiltar karamar hukumar Gwadabawa ta Kudu ya goyi bayan kudirin tare da bukatar dawo da wutar lantarki a wasu kauyukka da dama na kananan hukumomin Tureta da Dange Shuni.
Kauyukkan da dan majalisa ya zayyano dake fama da matsalar wutar sun hada da Kanfanin Ala, Lanbar Tureta, Kanfanin Diya, Bi-Masa Tasha, Bi-Masa Gari, Dorawa, Tureta Gari, Gidan Kare (a karamar hukumar  Tureta), sai  Bodai, Illelar Bissalam, Dabagi (a Dange shuni), da sauransu.
Randa ya sanar da majalisa matsalar wutar da mutanen ke fuskanta ta samu ne tsawon lokaci da batagari suka sace wayoyi da sauran kayan dake samar da  wuta.
"Lamarin ya kawo ci baya ga tattalin arzikin yankin in da masu kananan kasuwanci sun daina domin da wuta ne suka dogara.
"Haka matsalar tana shafuwar asibitoci da dakunan ajiyar magani, saboda yanayin zafi da ake fama da shi."
 
Dan majalisa ya koka kan lamarin in da Kankarar ta yi tashin gwauron zabo tsadar za ta Karawa magidanta nauyi a wannan Watan.
Ya ce yanayin saboda ana cikin lokacin zafi ne ake sayar da karamar kankara kan farashi naira 1000 ga duk daya.
Majalisar dokokin jiha ta hannun shugaban majalisa Honarabul Tukur Bala sun amince da kudirin tare da kira gwamnati ta gaggauta gyara matslar wutar a wuraren da lamarin ya shafa.