Sojoji sun kama  Ɗan Sanda Sajan da Harsasai 370 a Plateau

Sojoji sun kama  Ɗan Sanda Sajan da  Harsasai 370 a Plateau
Sojoji sun kama Ɗan Sanda Sajan da  Harsasai 370 a Plateau
 
Rundunar soji ta musamman ta Operation Safe Heaven (OPSH) ta ce ta kama wani dan sanda mai mukamin Sergeant da harsasai guda 370 a jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.
 
Jami’in hulda da jama’an rundunar, Ishaku Takwa ya bayyana hakan a wata takarda da ya saki a Jiya Alhamis.
 
Rahoton Jaridar The Cable ya bayyana Cewa Takwa ya ce sun kama dan sandan ne a jiya  Alhamis 17/09/2021 da rana a daidai kan titin anguwar Werreng dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar.
 
 Rundunar  ta ci karo da dan sanda tare da wani abokin harkar sa dauke da harsasai masu carbi guda 370,” kamar yadda takardar ta zo da bayanin.
 
 “Sun adana harsasan a wata mota kirar Toyota Pathfinder jeep mai lambar rijistar LGT 772 JN. 
 
“Asirin wadanda ake zargin ya tonu ne bayan direban ya yi yunkurin canja hanya daga matsayar sojin wuraren Werreng kan titin Barkin Ladi zuwa Jos. 
 
Sai dai motar ta ci karo da madakatar sojojin wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin su."
 
Takwa ya ce da aka tsananta bincike an gano cewa direban dan sanda ne inda ya kara da cewa sun mika gawarsa ga rundunar ‘yan sanda yayin da dayan yake shan tambayoyi, Kamar Yadda The Cable ta Ruwaito.
 
Sauran abubuwan da aka samu a hannun su sun hada da mota kirar Toyota Pathfinder, N205,000, daga, ma’ajin harsasai, tocila da wayoyi 3. An samu katin wurin aikin sa, daurin wata hoda da ake zargin wiwi ce da wata jaka da ake zargin kayan sawan su ne.