Zamfara Ta Sake Bude Wasu Kasuwannin Mako-Mako

Zamfara Ta Sake Bude Wasu Kasuwannin Mako-Mako
Gov. Matawalle

Zamfara Ta Sake Bude Wasu Kasuwannin Mako-Mako

 Daga Aminu Abdullahi  Gusau.


 A yau ne gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da bude wasu kasuwannin mako-mako, a wasu zababbun kananan hukumomin dake fadin jihar.

 Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai Alhaji Ibrahim Magaji Dosara kuma aka rabawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

 Sanarwar ta kara da cewa, "Muna  sanar da jama’a cewa, biyo bayan rahotannin samun zaman lafiya da  natsuwa a wasu  sassan jihar, da kuma jerin bukatu da jama’a suka yi na a sake bude wasu kasuwannin mako-mako, gwamnatin jihar ta yi nazari tare da amincewa da shirin.  sake buɗe kasuwannin mako-mako   daga yau litinin.

  "Kasuwan nin sun hada da Nasarawar Burkullu, Talata Mafara, Gusau, Shinkafi, Kasuwar Daji, Nasarawar Godel da Danjibga.

 "Sai dai gwamnatin jihar ba ta amince da sake bude kasuwannin dabbobi (kara) na wadannan kasuwanni ba.

 Hakazalika gwamnati ta yi gargadi kan duk wani abu na karya doka da oda a kasuwanni.

 Ta kara da cewa kada a ga mutane dauke da wani makami a cikin kasuwanni, haka kuma, kada a ga wani mutum yana kai hari ko barazana da sunan kowace kungiya.

 A bisa wannan sanarwar, an umurci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa mutane suna gudanar da harkokinsu na halal a cikin kasuwanni da kewaye ba tare da tsangwama ko tsoratarwa ba.

 Hakazalika an ja hankalin hukumar da aka kaddamar domin kiyaye dokar da gwamnati ta sanya na bin doka da oda, da su  tabbatar da bin ka'ida tare da kiyaye keta umarnin zartarwa.

 Gwamnati ba za ta yi jinkirin sake rufe duk wata kasuwa da aka samu tana karya odar." Inji  sanarwar.