2023: Buhari Da Tambuwal Sun Yi Ganawar Sirri  A Fadar Shugaban Kasa

2023: Buhari Da Tambuwal Sun Yi Ganawar Sirri  A Fadar Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal sun yi ganawar sirri a fadar shugaban kasa dake Abuja a Talatar nan.

Tambuwal yana cikin 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyar PDP mai adawa a Nijeriya.

Ganawar tare da Buhari ta zo ne bayan rikita-rikitar zaben wanda zai yi wa PDP takara ta hanyar silhu da ta shafi Tambuwal da sauran abokan tafiyarsa su uku a kudirinsu na fitar da dan takara ta hanyar  silhu.

Bangaren gwamnatin tarayya da gwamna Tambuwal har yanzu ba su fitar da wani bayani kan abin da shugabannin suka tattauna ba.

Da yawan wasu masana na danganta haduwar da wani sabon kudiri na Tambuwal kan neman mafita a siyasarsa.

Ana ganin a yanzu ba ya dasawa da gwamnan Rivers Wike ga wannan matsala da ta faru tsakaninsa da wasu dattawan Arewa dole ne ya nemi mafitar siyasarsa wanda hakan na iya kai shi da fadawa a jam'iya mai mulki ta APC.