Gwamnonin Kudu Har da Wike Sun Yi Matsaya Mulki Ya Koma Yankin a 2023----Gwamnan Ebonyi

Gwamnonin Kudu Har da Wike Sun Yi Matsaya Mulki Ya Koma Yankin a 2023----Gwamnan Ebonyi

 

Gwamnan jihar Ebonyi, Injiniya Dave Umahi, ya kalubalanci gwamnonin kudu da su fito su gaskata cewa baki ɗayansu suna bayan shugaban ƙasa na gaba ya fito daga kudu kamar yadda gwamna Wike ke fafutuka yanzu. 

A wata hira da kafar Talabijin ta Aris TV, Umahi ya bayyana cewa tun farko gwamnonin Kudu sun cimma matsayar cewa ya kamata a rika karɓa-karɓa da kujerar shugaban ƙasa. 
Haka nan kuma gwamna Umahi, mamba a jam'iyyar APC, ya musanta rahoton dake yawo cewa ya gana da gwamna Wike a Landan, inda ya kara da cewa yana nan matsayinsa na aboki. 
"Ban jima da dawowa daga tafiyar kwana Takwas ba daga Dubai kuma na karanta da kafafen watsa labarai cewa gwamna Nyesom Wike da wasu sun gana a Landan. Ban je Landan ba, hukumar shige da fice ta sani." 
"Wike ɗan uwana ne kuma aboki, mun ɗan samu saɓani kuma idan irin haka ta faru da yuwuwar a fusata ba ta har abada. 
"A baya mu manyan abokan juna ne har zuwa lokacin da na bar PDP." 
"Kun san cewa idan babban abokinka ya guje ka dole ka ji ba daɗi, amma mun sasanta da jimawa mun cigaba da abotarmu." 
Gwamna Umahi ya kara da cewa baki ɗaya gwamnonin kudancin Najeriya bakin su ɗaya, suna son a tabbatar da mulkin karɓa-karɓa ne a zaɓe mai zuwa. 
"Bari na faɗa muku, gwamna Wike da sauran gwamnonin kudu sun amince mulki ya koma hannun ɗan kudu kuma wannan ne ya hana PDP zama sakat duk da bana son magana kan wasu jam'iyyu." 
"Kafatanin gwamnonin kudu (Idan baku manta ba) sun zauna suka cimma matsayar a riƙa karba-karban kujerar shugaban kasa tsakanin kudu da arewa kuma ina ganin kowanensu yana girmama matakin." 
"Wike mutumin kirki ne, yana da zuciya mai kyau, mutum ne na gari, duk waɗan nan abubuwa ba daga karkashin zuciya suke fito wa ba, daga harshe ne yayin da ake cikin fushi."