Mahara Sun ƙi karɓar kuɗin Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

Yan bindiga a jihar Zamfara sun ki karbar kudin fansar da kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasir Magarya ya bada domin kubutar da mahaifinsa daga hannunsu.

Mahara Sun ƙi karɓar kuɗin Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

Mahara Sun ƙi karɓar kuɗin Fansar Mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara

Daga Falalu Lawal, Katsina

Yan bindiga a jihar Zamfara sun ki karbar kudin fansar da kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasir Magarya ya bada domin kubutar da mahaifinsa daga hannunsu.

An sace mahaifin Mr Magarya ne tare da wasu mutane biyar a wata Agusta yayin wani hari da aka kai kauyen Magarya a karamar hukumar Zurmi, kamar Yadda Premium Times ta Ruwaito..

Rahotanni sun ce wasu jami'an gwamnati sun tuntubi shugaban 'yan bindiga, Halilu Kachalla, ya taimaka musu wurin tattaunawa da 'yan bindigan da ke tsare da mahaifin kakakin majalisar..

Wani hadimin kakakin majalisar ya shaidawa Jaridar Premium Times cewa wasu jami'an karamar hukumar Shinkafi ne suka gayyaci Kachalla domin ya taimaka.

Ya ce magoya bayan kakakin majalisar a kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi suma sun tuntubi Kachalla nan take bayan sace mutanen.