Hukumar Zabe Ta Nijeriya Ta Saka Sabbin Ranakkun Zaben 2023

Hukumar Zabe Ta Nijeriya Ta Saka Sabbin Ranakkun Zaben 2023

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa waton INEC ta saka sabbin ranakkun zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya da gwamna da 'yan majalisar jiha a ashekarar 2023.

 

Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana cewa za a yi zaben shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya da suka kunshi sanatoci da 'yan majalisar tarayya a ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.  

Shigaban ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Asabar hakan kuma zaɓen gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi zai gudana ranar 11 ga watan Maris na 2023 ɗin.

A cewarsa, an zaɓi ranakkun zaben  saboda a tabbatar an yi aiki da sabuwar dokar zaɓe, wadda ta tanadi cewa wajibi ne a bayyana ranar zaɓen aƙalla kwana 260 kafin kaɗa ƙuri'a.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta wallafa sauran tanade-tanaden dokar zaɓen "a lokacin da ya dace".

A jiya ne shugaban kasa ya rattabwa sabuwar dokar zabe hannu abin da ake ganin zai samar da wasu sauye-sauye ga hukumar domin ganin an bi dokar yadda ta tanadar.