Gwamna Bagudu ya tallafawa kungiyar kwadago ta jihar Kebbi 

Gwamna Bagudu ya tallafawa kungiyar kwadago ta jihar Kebbi 


Gwamna Bagudu ya tallafawa kungiyar kwadago ta jihar Kebbi 

 

Gwamnan Kebbi Sanata Atiku Ababakar Bagudu ya aminta da fitar kudi miliyan biyar tallafi ga sabbin shugabannin kungiyar kwadago bangaren mata a jihar Kebbi.

Bayanin yana kunshe ne a cikin wata takarda da mukaddashin shugaban ma'aikatan jihar Alhaji Safiyanu Garba Bena ya fitar bayan ya sanya hannu a ranar Assabar data gabata a birnin Kebbi.

A cewar bayanin gudunmuwar da gwamnan ya bayar ga sabbin shugabannin kungiyar a gefen mata domin aiyukkansu na jinkan jama'a da shirya tarukka na horaswa da koyar da mambobin kungiyarsu sana'o'in hannu dake kara tallafawa mutum.

Gwamnan ya taya sabbin shugabbanin kungiyar kan zabarsu da aka yi da yi masu fatan kammala wa'adinsu cikin nasara.

Sabbin shugabannin sun yi farinciki da wannan tallafi domin a cewarsu zai taimakawa aiyukkan kungiyar da suka sanya a gaba.