Soja ya caka wa ɗan sanda wuka har lahira a Jalingo

Soja ya caka wa ɗan sanda wuka har lahira a Jalingo

An zargi wani sabon soja da aka ɗauka aiki, Dauda Dedan,  da caka wa ɗan sanda mai mukamin constable, Aaron John, daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Taraba, wuka har ya mutu a birnin Jalingo.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, James Lashen, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Jalingo ranar Laraba, inda ya bayyana cewa hakan ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a ranar Litinin a unguwar Mayo-Goyi, da ke wajen birnin Jalingo.

Lashen ya ce marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da wata hatsaniya da ta ɓarke tsakaninsu da sojan, inda daga bisani lamarin ya rikide zuwa tashin hankali har ya kai ga an cakawa sojan wuka.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya bayyana cewa sojan ya tsere bayan faruwar lamarin, amma sojoji sun fara bincike kuma sun tabbatar wa ‘yansanda da za su kamo wanda ake zargin domin ya fuskanci hukunci.