Tsaro: Dan Bindiga Bello Turji bai aje makami ba--Sakkwatawa

Tsaro: Dan Bindiga Bello Turji bai aje makami ba--Sakkwatawa
Maganar jingine makami da karbar sulhun zaman lafiya da babban dan bindiga Bello Turji aka ce ya yi, masu biyar harkokin tsaro a yankin Sakkwato sun karyata lamarin.
Masanan sun ce ba a yin sulhu irin wannan cikin daki ba tare da duniya ta san halin da ake ciki, don sanin sharuddan da aka gindaya a tsakanin hukuma da dan bindigar.
Alhaji Bashar Altine Guyawa wani mai sharhi ne kan lamurran tsaro a Sakkwato maganar da ake yadawa kan sulhu da dan bindiga Turji ba kamshin gaskiya a ciki, "karya ce da dauke hankalin jama'a". 
Bayanan da ake yawo da su a kwanan nan an ce dan bindiga Bello Turji ya ajiye makamansa ya karbi sulhu biyo bayan tattaunawa da aka yi tsakaninsa da wasu malaman addini a mabuyarsa da ke dajin Fakai a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Altine ya tabbatar Turji yana cin karensa ba babbaka a Gabascin Sakkwato da makwabciyar jihar Zamfara.
Ya ce Turji da yaransa suna ci gaba da tarwatsa da kashe manoma a garuruwa daban-daban.
"Turji bai mika wuya ba, hasalima mutanensa sun fi kai hare-hare, a kwana 50 kadai kauyukka 34 ya sanyawa harajin zaman lafiya ya tilasta su sai sun biya sama da miliyan 100 kafin ya bar su su yi noma a gonakkinsu a wannan daminar ta bana."
Ya ce "harajin ana karbar shi ne bisa tsarin dole da Turji ya sanya ga mutanen Isa da Sabon Birni na jihar Sakkwato, sai shinkafi ta jihar Zamfara.
Altine Guyawa ya bayyana kudin da suke biya matsayar dan bindigar ne kan ko su biya kudin ko su yafe noma a wannan shekara, abin da zai iya kawo karancin abinci.
Ya kara da cewa Turji a sansanin Gwali-Gwali yana rike da mutane da ya yi garkuwa da su tsakanin mutum 85 zuwa 150 ya kamo su a gabascin Sakkwato da makwabtan garuruwa kamar Fakai da Dangwamdai da Tsaika.
Guyawa ya gargadi masu yada Turji ya mika wuya hakan na iya kawo sanyin guiwa ga al' ummar dá ke kokarin kare 'yan ta'addan da ke kawo hari.
"Yakamata mutane su san abin da za su yarda da shi har su yada, watsa Turji ya ajiye makami zai taimake sa yakai hari salin alim mutanen da yake kaiwa harin za su cigaba da shan wuya.
Majiya ta tsaro a yankin ta tabbatar a hukumance ba bayanin Turji ya ajiye makaminsa don haka mutane su jira sai irin wannan bayani ya fito hannun hukuma Sannan a aminta da shi.
Malam Murtala Asada ya bayyana cewa magannar an fito da ita ne don a yi wa Turji mafita tun da shi ɗan sako ne.
"Abin mamaki ne malamin addini ya yi karya ya ce Turji ya yi surrender, ya aje makamai, duk wanda ya fadi haka makaryaci ne, Turji bai aje makami ba, kwana uku a jere a wannan satin sai da Turji ya kashe mutane, akwai Yusuf Maicaji a Isa da Bello Turji ya kashe."
Ya ce  munafunci ne ke wahalar da Arewa,  kariyar Turji mai kashe mace da juna biyu ya farke cikinta ya fitar da jariri bai da wani abu mai kyau da har wani zai kare shi, har ya kawo matsalar su ya ce ta manoma da makiyaya ce.
"Yanzu haka akwai mutanen Shinkafi hannun Bello Turji da yake tsare da su akwai wani Maniru da Nura da Kabiru da Muhammad da Zainab da Jummai an kai kudin fansar su amma Turji ya rike su duk wadan nan mutanen Shinkafi ne," kalaman Murtala Asada.