Hana Matashi Sallah  Ya Sa Ya Hakura da Aikin da Yake Yi a Kamfani

Hana Matashi Sallah  Ya Sa Ya Hakura da Aikin da Yake Yi a Kamfani

 

Mun samu labarin wani matashi wanda ya ajiye aikinsa saboda dalili guda, an hana shi damar da zai rika bautawa Ubangijinsa. Katsina Post ta rahoto Malam Abdullahi Sulaiman yana mai cewa ya hakura da aikin da yake yi, saboda ya samu damar yin ibada da kyau. 

Abdullahi Sulaiman yace ana hana shi yin sallah a kamfanin da yake aiki a garin Legas, ganin halin da ya samu kan shi, sai ya bar aikin.
Rahoton yace wannan Bawan Allah ya fito daga karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, ya kuma tafi Legas da nufin samun na abinci. 
Da zarar matashin ya tashi zai yi sallah, sai manyansa su hana shi, su fada masa cewa ya dakata tukuna sai ya tashi daga wajen aikin na sa. 
Malam Sulaiman wanda aka fi sani da Abulali Kankara yana aiki ne lokacin a wani kamfanin mai da ke garin Legas mai suna Nest Oil PLC. 
"Aiki ne nake yi a wani kamfanin mai na Nest oil a nan Legas. Duk lokacin da na nemi su bani dama na je nayi sallah sai su ce a’a…