Honarabul Kabir Tukura, Ya Tabbatar Da Kudurinsa, Wajen Samar Da Harkokin Kasuwanci Da Inganta Makarantu, A Mazabunsa
Tukura ya sanar da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki tukuru tare da gwamnatin jihar kebbi, wajen inganta makarantu da kuma hanyar madatsun ruwa duk dai domin bunkasa harkokin kasuwanci da ilimi a wannan yankin, Tun da farko dai shuwagabannin yan kasuwa da Malaman makarantu sun bayyana cewa Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, yana aiki tukuru kuma sun yaba mishi bisa kokarin sa na samar da hanyoyin kasuwanci a cikin babbar kasuwar Zuru, da kuma ingattaccen ilimi wanda hakan ya baiwa masu harkokin kasuwanci damar yin kasuwanci su acikin lumana, Shuwagabannin yan Kasuwa na cikin garin Zuru sun yi kira ga Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya yayi burus da masu adawa bisa irin ayyukan raya kasa, da cigaban al'umma da yake yi a fadin Zuru, inda suka ce babu wata nasara da take tabbata ba, tare da mahassada ba,
Honarabul Kabir Tukura, Ya Tabbatar Da Kudurinsa, Wajen Samar Da Harkokin Kasuwanci Da Inganta Makarantu, A Mazabunsa,
Daga Abbakar Aleeyu Anache,
Dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba da ke jihar kebbi Honarabul Kabir Ibrahim Tukura kana Shugaban Matasan'yan majalisun Najeriya, haka zalika kwamitin Sharia a Najeriya,
Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya tabbatar da Kudurinsa wajen gyarawa da samar da tituna a wannan yankin domin kara bunkasa harkokin kasuwanci da kuma fannin ilimi,
Tukura ya sanar da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki tukuru tare da gwamnatin jihar kebbi, wajen inganta makarantu da kuma hanyar madatsun ruwa duk dai domin bunkasa harkokin kasuwanci da ilimi a wannan yankin,
Tun da farko dai shuwagabannin yan kasuwa da Malaman makarantu sun bayyana cewa Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, yana aiki tukuru kuma sun yaba mishi bisa kokarin sa na samar da hanyoyin kasuwanci a cikin babbar kasuwar Zuru, da kuma ingattaccen ilimi wanda hakan ya baiwa masu harkokin kasuwanci damar yin kasuwanci su acikin lumana,
Shuwagabannin yan Kasuwa na cikin garin Zuru sun yi kira ga Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya yayi burus da masu adawa bisa irin ayyukan raya kasa, da cigaban al'umma da yake yi a fadin Zuru, inda suka ce babu wata nasara da take tabbata ba, tare da mahassada ba,
Tukura, ya kara tabbatar wa al'ummar Zuru, Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba, kamar yadda aka sani yana da Manufofi wadanda kai tsaye takan duba aihin bukata na al'umma na musamman abunda ya shafi inganta ilimi da kasuwanci,
Kuma za'a cigaba da bada dukkan goyon baya don ganin an yi yaki da talauci wajen tallafawa Matasa da ayyukan yi wanda zai bada damar sauke nauyin dake kanmu,
Tukura, ya kuma bukaci wadanda suka ci moriyar wadannan ayyuka da su yi amfani da wannan damar wajen inganta rayuwarsu,
managarciya