Ambaliya ta mamaye kauyukka 3 ta raba mutane masu yawa da muhallansu a Sakkwato

Ambaliya ta mamaye kauyukka 3 ta raba mutane masu yawa da muhallansu a Sakkwato
A kalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato, suna bukatar agajin gaggawa da tallafi daga wurin mahukunta.
Ambaliyar da ta mamaye kauyukkan garin Tangaza da Gidan Madi da Baidi da Madarare ta haifar da faduwar gidaje da lalacewar Gonakki da rijiyoyi da sauransu.
Magidantan da lamarin ya shafa suna bukatar abinci da magani da tsaftatattun ruwa.
Shugaban karamar hukumar Tangaza Isah Salihu Kalenjeni ya jagoranci wata tawaga sun ziyarci wuraren da lamarin ya shafa don ganin barnar da ruwa suka yi, da jajantawa.
A lokacin ziyarar ya tabbatarwa mutanen zai sanarda duk wata hukuma da ta dace don kawo masu daukin gaggawa a halin da suke ciki.
Hukumomi a karamar hukuma da masu bayar da agajin gaggawa  an yi kira gare su da su yi aiki tukuru don kare barkewar annobar ciwo ga sauran al'umma.
Aliyu Na Abba ya samu hasarar gidansa da gona biyu ya ce yana bukatar hukuma ta tausaya masa yana cikin halin damuwa ga shi da iyalansa sun rasa wurin labewa ga kuma hasarar kayan noman da suka yi a taimaka musu.
Umaima Dan Umaru da ta ke da marayu uku a tare da ita ta ce ginar gidansu ta fadi sanadin ambaliyar nan, gonarsu biyu da suka yi shuka sun lalace ruwa ya bata komai gero da waken da suka shuka ya lalace, suna neman dauki a taimaka masu da halin da suke ciki.
Ta ce mutanen da suka samu hasara sun fi hamsin a yankinsu kawai na Tangaza.