Tinubu@70: Kai Jagoran Jagorori Ne---Ahmad Lawan 

Tinubu@70: Kai Jagoran Jagorori Ne---Ahmad Lawan 

 
Daga Awwal Umar Kontagora, a Abuja.
 
 
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya taya jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekaru 70 da haihuwa. 

Lawan ya bayyana Asiwaju Tinubu a matsayin ƙwararren masanin mulki wanda ya kafa turbar zamanantar da jihar Legas, kuma shugaban siyasa da ya shahara wajen gina mutane da ƙungiyoyi. 
Mista Ola Awoniyi mai baiwa shugaban majalisar dattawa shawara akan aikin jarida ne ya fitar da sanarwar ga manema labaru a Abuja.
Yace, "ina mai taya jagoran jam'iyyar mu, Asiwaju Tinubu murnar zagayowar ranar haihuwar sa. 
"Ina mai bin sahun dangin sa, abokan sa, abokan siyasar sa da masu masa fatan alkhairi a ciki da wajen Nijeriya wajen taya shi murnar cin ma wannan zango na rayuwa a cikin ƙoshin lafiya. 
"Asiwaju Tinubu yai rayuwa ta hidimta ma jama'a, ta inda ya inganta rayuwar jama'a da dama a tsawon shekarun da yayi yana siyasa da aikin gwamnati. 

"Wannan yasa shi ya kasance a matsayin jagora a siyasa, jagoran jagorori kuma gwarzo a lokacin rayuwar sa. 
"Ya kasance a yau ba wai kawai wani babba da ake damawa da shi a siyasar Nijeriya kawai ba, amma ɗaya daga cikin muhimman al'amuran ƙasar nan. 
"Ina ma Jagaban Borgu fatan ƙarin shekaru a nan gaba don ya cigaba da hidimta ma Nijeriya da jama'ar ta".