Sanata Lamiɗo ya ɗauki nauyin karatun jami'a ga marayun yankinsa
ba mu da matsala da namba ko adadi komai yawan wadanda suka cancanta za mu tura su domin burina duk abin da na samu na kashe shi a wurin taimakon al'umma.
Sanata Ibrahim Lamiɗo dan majalisar dattijai mai wakiltar yankin Sakkwato ta gabas ya ɗauki nauyin karatun jami'a ga marayu maza da mata da suka fito yankinsa.
Sanata Ibrahim Lamiɗo a karkashin gidauniyarsa ta bayar da ilmi, an soma tantance marayun a satin da yagabata kan haka ya yi karin haske ga manema labarai jim kadan da soma aikin.
"Ina cikin godiyar Allah zuciya ta na cikin farin ciki, in kana da hali ka taimaki matashi domin Allah ne kadai ya san wanda zai taimaki al'umma.
"Naji dadin matasan da na tura karatu kasar Indiya don na samu labarai masu kyau suna cikin koshin lafiya, suna karatu a cikin yanayi mai inganci na kulawa, sai godiyar Allah, hakan ne ya kara min kwarin guiwa sake tura wasu matasa a jami'ar Maryam Abacha don su ma su amfani rayuwarsu,"Kalaman Sanata Lamido.
Kan yawan daliban da zai tura Lamido ya ce "ya danganta da gurabun da makarantar ta ba mu, a lokacin da muka yi na Indiya mun so mu fara da dalibbai 60 zuwa 70 amma daga karshe suka aminta mu tura 44, shi ma wannan ya danganta, ba mu da matsala da namba ko adadi komai yawan wadanda suka cancanta za mu tura su don su yi digiri na farko, burina duk abin da na samu na kashe shi a wurin taimakon al'umma.
"Wadanda za mu tura a yanzu diyan marayu ne da aka kashewa iyayye a matsalar tsaron yankin Sakkwato ta Gabas, na shirya daukar nauyin karatunsu gaba daya," a cewar Sanata Lamido.
managarciya