Tambuwal ya kira taron tsaro a jihar Sakkwato

Tambuwal ya kira taron tsaro a jihar Sakkwato

Tambuwal ya kira taron tsaro a jihar Sakkwato

Gwamnan jijar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya kira taron masu ruwa da tsaki kan tsaro  a jihar domin gano bakin zaren harkar tsaron dake addabar ƙananan hukumomin jihar musamman yanki Sakkwato ta gabas.
Managarciya ta yi kiciɓis da takardun gayyatar muhimman mutane da aka riƙa rabawa daga ofishin sakataren gwamnatin jiha don neman su halarci taron.
Wata majiyar ta shedawa Managarciya cikin mutanen da aka gayyata har da jagoran jam'iyar adawa ta APC Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kuma ya nuna sha'awar halartar taron da yake ganin yakamata a kira tun kafin yanzu da lamurran suka ƙara rincaɓewa.

Matsalar tsaron jihar na cikin matsala musamman a yankin Sabon Birni da gari sama 20 aka tayar da su wasu sun koma Nijar gudun hijira, yayin da suke cikin wahalar rayuwa.

Ɗayan ɗan majalisa mai waƙiltar Sabon Birni Aminu Ibrahim Boza ya nuna takaicinsa kan yanda gwamna ya fita batun harkar tsaron jiha duk da al'ummarsa na shan wahala da rasa rayukkansu hannun mahara.