JUYIN MULKI: KUNGIYOYIN MATA A NIJAR SUN YI TARON ADDU'O'IN NEMAN MAFITA
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
A Ranar Litinin da ta gabata, Wasu Kungiyoyin Addinin Musulunci na mata, a Maradi , Jamhuriyar Nijar, karkashin jagorancin Malama Khadija Abubakar Maradi, sun gudanar da taro na musamman akan yanayin da kasar ta ke ciki.
A lokacin Taron, angudanar da Adduoi na musamman dan samun saukin yanayin da kasar take ciki, kana Shugabar, tayi Karin bayani akan dalilin Kiran taron inda ta bayyana cewa sun ja hankalin Yan uwa akan illolin Yaki, musamman mata da kananin Yara wadan da sun fi kowa wahada, kana sunyi kira ga Yan siyasa da sojojin cewa su Sani Allah ke baiwa mulki ga Wanda ya so a lokacin da yaso dan haka, komai a Maida shi ga Allah, ta Kara da cewa sunyi tuni ga kungiyar ECOWOS da CEDAWO cewa su Sani an Samar da kungiyar ne dan inganta Tattalin Arzikin kasashen, ba an Samar da su ne dan kuntatawa Alummah , ko Yaki ,kana su yi kokarin yin sulhu maimakon Yaki, ko daukar matakan tsaurarawa duba da yadda aka rufe boda da Kuma takurawa Yan kasa musamman ga shi ko kudi baa fitarwa ta banki yadda ya kamata ,su tuna akwai maras lafiya da maras Hali da ke cikin yanayin lahaula.. " a can da munasayen Buhun Shinkafa Jikka goma da Rabi zuwa Sha Daya,amma yanzu ta Kai Goma Sha Biyar zuwa Sha Shidda ...." injita..."wannan gun Ina dumurkuradiya", kana sunyi adalci duba da yadda aka tsaurarawa kasar sabanin sauran kasashen da ba haka akayi masu ba dan haka, muna tuni, da Suji Tsoron Allah,suyi adalci, Haka Kuma anyi kira ga malammai da su dukufa ga Tunatarwar da ya kamata ayi cikin wannan halin, da Kuma tunatar da Alummah a tuba a koma ga Allah, kungiyar Wadda bata siyasa ce ba, ta addini ce ta taimakon Yara marayu, uwayen marayu da zawarawa, ta Yi kira ga masu Watsa labarun karya da cewa su Sani duk abin da ka yada sai Allah ya tambaika.
"dan haka Yan social media aji tsaron Allah , adai na iza labarin da ganin shi batare da tantancewa ba " Malama khadeja ta bayyana Jin dadin su da godiya ga makwaftan kasashe akan muna damuwar su da Addu'ar da suke yi masu, " musamman Yan uwan mu na Najeriya" Sun bada tabbacin cigaba da gudanar da Addu'oin har Allahbya kawo dauki.
managarciya