Sabon Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje

Sabon Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Kwankwaso Da Ganduje
Lokacin da Ganduje ya kai wa Kwankwaso ziyarar ta'aziyyar rasuwar ƙaninsa a kwanannan dai-dai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yin sulhu tsakanin tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da magajinsa gwamna mai ci Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wani sabon rikicin siyasa ya sake kunno kai tsakaninsu.
Yayin wata hira da jaridar Punch Kwankwaso ya bayyana nasarar da Ganduje ya samu a zaɓen 2019 a matsayin haramtacciya, yana cewa wasu gaggan 'yan siyasar jam'iyyar APC ne daga sama suka ƙaƙaba wa al'ummar jihar Kano shi.
''Muna da ƙarfin da za mu iya hana su abun da suka so yi a wannan lokaci, amma sai muka yi la'akari da cewa idan muka biye musu hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, don haka muka bar su da aniyarsu, muka bi matakin shari'a, amma a nan ma aka yi abun da aka yi'' in ji Kwankwaso.
To sai dai wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin jihar Kano mai ɗauke da sa hannun kwamishinan watsa labaran jihar Muhammadu Garba, ta bayyana kalaman na Kwankwaso a matsayin shaci faɗi da ko kaɗan babu ƙanshin gaskiya a cikinsu.
''Abun takaici ne yadda  matsayin Kwankwaso na shugaba, wanda ake damawa da shi a harkokin gudanar da zaɓe ya kasa amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma mai zaman kanta ta gudanar kuma kotu ta amince da shi'' in ji Sanarwar.
Gwamnatin ta Kano ta ci gaba da cewa hirar da Kwankwason ya yi da jaridar Punch ta janyo masa mummunar illa ne fiye da alfanun da ya yi tsammanin za ta haifar masa.
Wasu na danganta waɗan nan kalamai da sabuwar rigima ce ta kunno kai a tsakaninsu in da wasu ke ganin sam ba haka ba ne.