Ƴan majalisar 3 sun fice daga PDP zuwa APC a Kaduna 

Ƴan majalisar 3 sun fice daga PDP zuwa APC a Kaduna 

Mambobi uku na majalisar dokokin jihar Kaduna da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP sun APC.

'Yan majalisar sun bayyana cewa sun yanke wannan shawara ne sakamakon “kyakkyawan shugabanci” da gwamnan Kaduna, Uba Sani, ke gudanarwa, wanda ya sa suka bar PDP don su shiga APC.

Mambobin majalisar ukun sun hada da Henry Mara (mazabar Jaba), Emmanuel Kantiok (mazabar Zonkwa), da Samuel Kambai (mazabar Zango). Sun sanar da sauya shekarsu a ranar Alhamis ta cikin wata wasika da suka aika wa mazabunsu.

'Yan majalisar sun bayyana cewa sun yanke shawarar komawa jam’iyya mai mulki a jihar domin kare muradun al’ummarsu tare da tabbatar da cewa sun fi samun wakilci nagari a cikin APC.

Henry Mara, wanda shi ne shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, ya ce “shaharar da rinjayen PDP a kudancin Kaduna sun rushe” sakamakon nasarorin da gwamnan ya samu wajen kawo zaman lafiya da hadin kai.

“Babban sauyi a tsarin karfin iko na majalisar dokoki yana gabatowa, domin muna sa ran karin ‘yan adawa za su bar PDP su koma APC,” in ji Mara.