Kotu Ta Saukar Da   Shugabannin  APC A Bauchi

Kotu Ta Saukar Da   Shugabannin  APC A Bauchi

 

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar, rahotanni sun baiyana cewar shi dai shugaban yaron Ministan Ilimi ne,  Malam Adamu Adamu.

 

A ranar 16 ga watan Oktoba ne dai wasu magoya bayan jam'iyar su ka nuna rashin amincewa da zaɓen shugabannin APC da Misau ya lashe, inda hakan ya jawo rabuwar kawuna a jam'iyar reshen jihar ta Bauchi.

 
Hakan ya sanya  fusatattun  suka kai ƙara kotu, da roƙon a soke zaɓen sakamakon maguɗi da suka ce an yi da kuma ƙaƙaba ɗan takara da wasu "'yan siyasar Abuja" su ka yi.
 
A takardun ƙarar da jaridar Daily Nigerian ta samu, ta gano cewa wani Hassan Mohammed Sheriff ne ya shigar da ƙarar, inda ya nemi kotun da ta rushe shugabacin jam'iyar, ƙarƙashin Misau.
 
Ƙarar da a ka kai kotu ta haɗa da shugaban jam'iyar na riƙon ƙwarya na ƙasa, Mai Mala Buni, Shugaban Kwamitin Masu ruwa da tsaki na jam'iyar a Bauchi, Adamu Adamu da kuma mamba a kwamitin masu ruwa da tsaki, Yakubu Dogara, da sauran mutane 39.
 
Alƙalin kotun, Kunaza Hamidu, ya baiwa Misau da shi da sauran shugabannin jam'iyar da kada su ƙara nuna kan su a matsayin shugabannin jam'iyar har sai kotu ta saurari kowanne ɓangare ta kuma yanke hukunci.
Rikicin jam'iyar APC yana kara ta'azara a jihohi da dama gashi kuma ana tunkarar babban zaben shugabannin jam'iya a kasa.
APC ta fada rikici wanda kusan an kasa gane makamarsa abin da ba saban ba a ga jam'iya mai mulki ta fada a rikicin shugabanci.