Babban Buri:Fita Ta Sha Bakwai

Fizgar motar ya yi a sukane ikon Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, ko saita parking ɗin motar beyi ba ya yi cikin part ɗin Alh Bello da saurinsa. Cilli ya keyi da duk abinda ya gani gabansa gaba ɗaya idanuwansa sun rufe baya ganin komai a lokacin muradinsa kawai yaci karo da tukunyar da aka faɗa masa. Ɗakin ya faɗa ya yi wurgi da katifar dake kan gadon sannan ya janyo karagar gado itama ya yi cilli da ita.

Babban Buri:Fita Ta Sha Bakwai

BABBAN BURI


MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.

FITOWA TA SHA BAKWAI


~~~"Nasan baza su taɓa gayama ba" , nan ta hau gaya masa irin ta'asar da su kayi kana daga ƙarshe tace "kaje bayan gida gurin shuke shuke suke dai dai iccen mangoro ka duba da kyau zaka ga rame a gurin ba kowa yasan da gurin ba sai wamu wamu shi'isa zaka gane gurin da abin yake, ka tone ramen zaka ga layu guda uku a ciki , ka tabbatar ka ƙone su insha Allahu duk inda ALIYU yake zai dawo gida, sa'annan ka shiga da kanka cikin ɗakin Alh a ƙarƙashin gadonsa zaka ga tukunya , ka tabbatar ka fasa tukunyar zai dawo hayyacinsa domin kuwa duk inda yake tun daga ranar daya ɓata baya cikin hankalinsa gaba ɗaya anshafe masa komai dake cikin kwakwalwar sa, sunan sa kawai zai iya faɗa daga shi ba wani abu daya sani koya iya.

Runtse idanuwansa ya yi jikinsa har rawa yake yi ya nufi hanyar waje ba tare daya ce da'ita komai ba.

Yana buɗe ƙofar ɗakin suka ci karo da Alh Bello yana sanyo kai cikin ɗakin, ba tare daya bi takansu ba ya yi waje da sauri.

Fizgar motar ya yi a sukane ikon Allah ne kawai ya kaishi gida lafiya, ko saita parking ɗin motar beyi ba ya yi cikin part ɗin Alh Bello da saurinsa.
Cilli ya keyi da duk abinda ya gani gabansa gaba ɗaya idanuwansa sun rufe baya ganin komai a lokacin muradinsa kawai yaci karo da tukunyar da aka faɗa masa.

Ɗakin ya faɗa ya yi wurgi da katifar dake kan gadon sannan ya janyo karagar gado itama ya yi cilli da ita.

Gaba ɗaya sai da ya mayar da gadon wayam ya rage tukunyar nan ce kaɗai a jiye a gurin , waƴansu ruwa ne a ciki kalar miyar kuka da ganinsu ba zasu rasa ɗoyi ba gaba ɗaya tukunyar ta koma green ba kyaun gani.

Hannu biyu yasa ya ɗauko tukunyar da bisimillah a bakinsa, sannan ya fito a ɗakin idanuwansa sunyi jazur dasu , numfashi yake fitarwa da sauri sauri , kai tsaye bayan gida ya nufa ya watse tukunyar a ƙasa.

A dai dai lokacin muna kauyen ƙiri garin mahaifiyata kenan, da yake tun safe aka bugowa Babanmu waya kan cewa Kakanmu wato mahaifin Mama yana nemansa damu gaba ɗayan mu.

Hakan ya sanya da sanyi safiya muka ɗunguma dukanmu muka nufi ƙiri.

Muna zaune a gaban Kakan mu yayinda Baba ke kusa dashi suna magana kai da kanka daka gansu zaka tabbar da maganar sirri ce.
Harna kai bakin ƙofa da niyar na fice daga ɗakin ina riƙe da hannun Ahmad sai kawai naga Baba ya riƙe kai lokaci ɗaya haɗi da sakin wata gigitacciyar ƙara lokaci ɗaya ya zube a gurin kamar ba rai a tare dashi.

A dai dai lokacin ne Haidar ya fasa tukunyar ya nufi ramen da akace masa domin ya tone sa.

Da gudu na isa gurinsa ya yinda Mama da matar Kakanmu dashi kansa Kakanmu suka rufamin baya.

Ganin kamar ba rai a jikinsa ya saya ni zubewa a gurin ban koma sanin inda kaina yake ba sai bayan mintoci.

Har lokacin Kakanmu na iya ƙoƙarin sa domin ganin Baba ya farfaɗo amman inaaa kamar babu shi.

Zuwa lokacin kowa dake ɗakin kuka ya keyi idan ka cire Mama da Kakanmu , miƙewa ya yi ya nufi wani galam dake ajiye cike da ruwan rubutu , karkata shi yayi ya tara kofin hannunsa ruwan rubutun suka zuba bada yawa ba a cikin kofin ya mayar ya rufe galam ɗin kana ya dawo ya ɗaga Baba dake kwance kamar gawa ya buɗe bakinsa ya ɗiga masa ruwan a ciki, sannan ya kwantar dashi ya wanke masa fuskansa da ruwan nan.
Mu dai kallo kaɗai muke biyansu dashi.

Lokaci ɗaya muka ga Baba ya miƙe zaune waƴansu maganganu da bamu san na miye ba.
"Murtala Bello dan girman Allah karku aiwatar kar kuyi ku faɗi duk abinda kuke buƙata zamu baku amman dan Allah karku aikata".

Sosai hankalin mu ya tashi domin kuwa a zuri'ar mu kaff ba Bello balle Murtala.

Ruwan rubutun ya koma kafa masa a baki yana faɗan "yi bisimillah kasha wannan ALIYU".

Kallon sa ya yi sannan ya ɗago yana kallonmu sannan ya ce "inane nake nan?, waye ku?.

Kuka naji Mama ta fashe dashi me tsananin ƙarfi kai dajinsa kasan daga ƙasan rai yake.

Kallonta Kaka ya yi sannan ya ce "meye haka kuma?, da girman ki?, godiya ya kamata kije kiyiwa Allah ba kuka ba tun yaushe muke jiran wannan ranar?, ai kuwa tunda Allah ya nufi muka ganta ba abinda zamuyi sai gode masa".

Sosai Baba ya kafe Mama da idanuwansa yana biyanta da kallo.
Sannan ya kalli Kaka ya ce "malam ku zuwa ye dan Allah?".
"Ka kwantar da hankalin ka yanzunnan zanyi ma bayanin komu su waye.
Gyaɗa kansa ya yi alamar gamsuwa.

Ni dai cike da ɗunbin mamaki nake kallonsu na rasa fahimtar ina zancen su ya nufa, gaba ɗaya ban fahimci kalma ko ɗaya daga cikin maganar da suke yi ba.

★★★★★★

Ganin layu uku da ya yi ne yasanya sa da karawa daga tunar ramin da yake yi sannan ya mayar da ƙasar kamar yadda ya ganta ya rufe.

Kai tsaye sashen Hajiya Inna ya nufa ya ɗauko a shana ya hasa wuta ya babbake su sannan ya kwashe tukar ya kai cikin ruwan dake gudana ya zubar sannan ya dawo sashen Hajiya Inna.

Ta fito daga kitchin sai kawai ta ci karo dashi zaune duk ya canja cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
"Shalele lafiya kuwa?".

Miƙewa ya yi yaje ya rungume ta sannan ya ce "insha Allahu Hajiya Inna ɗanki ya kusa dawowa gareki , yanzunnan na kammala tone duk wani sharri nasu a cikin gidannan.

Kallonsa ta yi cike da alamun tambaya sannan ta ce "meke faruwa?".

Janta ya yi ta zauna shima ya zauna sannan ya zayyane mata komai da komai da mga ƙarshe ya haɗa da "insha Allahu *BABBAN BURI* na ya kusa cika , mahaifina ya kusa dawowa gareni ku kuwa azzalummai yanzu kanku zan dawo".

Sosai Hajiya Inna ta yi farin ciki harda kuka ta yi sannan ta ce "bara na tashi zuwa yiwa autana girki kenan".

"Wannen girki kuma Hajiya Inna ki dai zauna ki huta yafi domin kuwa baki san har wane gari suka wurga shi ba, kuma kiyi addu'ar Allah yasa yananan da ransa".

"Jikina na bani ɗana ALIYU da ransa insha Allahu yananan bayyana a gareni yau ko gobe".


★★★★★★

Kallonsa Malam Ibrahim ya yi wato Kakanmu sannan ya ce "Alhamdulillah tsawon lokacin daka ɗiba baka cikin hankalinka yanzu a ƙalla anyi shekaru ashirin da biyar yanzu haka.

Ina tafe a gona ta ina ban ruwa ni da yaron wajena wato Haladu, harmun kai ƙarshen gona zamu jirkita mu koma sai kawai na tsinkayo mutum kwance tsakanin gonata data makwabcina da hanzarinmu muka nufi gurin muna masu gyara ma kwanci sa kasan cewar a jicce kake kwance, tsayawa muka yi muna ƙarema kallon rashi sani muka yi kamin daga bisani na sanya ruwa na shafema fuskarka da ruwan addu'a, ka ɗan jima kamin ka farfaɗo na tambaye ka sunan ka kace ALIYU nace daga ina kasancewar ban taɓa ganin ka ba, kayi shuru duk tambayar dana yima shuru a haka makwabcina yazo ya tadda damu , na tambayesa ko yasan ka yace "a'a" a tare muka koma da kai gidana a ranar, margayiya mahaifiyar Saudatu itace ta tarbemu , saida muka nutsu nake yi mata bayanin ka , cike da tausayawa take kallon ka.

In taƙaitama lokacin gana ɗaya ba abinda ka iya hatta sallah baka san yadda akeyinta ba, anan na zauna dakai tsawon wata ukku ina koyar da kai komai da komai na malam bahaushe sannan da addinka , bayan shekaru sunja naga zamanka a haka bame yi bane , muka yanke shawarar aurama ƴata Saudatu wacce muka haifa da magajiya ita kaɗai Allah ya bamu.

A haka kuke zaune a cikin garinnan sai daga bisani kuma kuka koma cikin gari da zama domin neman abinda zaku dinga sawa a bakin salati.

Shekarar ku biyu da aure Allah ya azurta ku da ƴa macce wacce taci sunan Khadeejah ga tanan ya faɗa yana me nuno ni da hannu, bayan ita kuma haifi A'isha daga ita sai Umar sannan Ahmad su huɗu Allah ya albarkace ku da haihuwa.

Nan dai Malam ya yi ta sanar da Baba abubuwa da dama waƴanda suka danganci rayuwarsa ta baya.....


Za mu cigaba a gobe.....


ƳAR MUTAN BUBARE CE