Rikicin Tambuwal da Kwankwaso:PDP ta ɗage taronta na yankin Arewa-Maso-Yamma

Rikicin Tambuwal da Kwankwaso:PDP ta ɗage taronta na yankin Arewa-Maso-Yamma

 

Kwamitin Zartarwa na Jam'iyar PDP ya ɗage taronta na yankin Arewa-Maso-Yamma, wanda aka sa ranar yin shi a gobe Asabar 12 ga watan Fabarairu 2022.

 

Hakan na kunshe ne a wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa, Umar Muhammad Bature.

 
Ya ce jam'iyar za ta sanar da sabuwar ranar da za ta yi taron nata, inda ya shaidawa hukumar zaɓe, 'yan takara da wakilan zaɓe da ma duk masu ruwa da tsaki a cikin sanarwar da ya fitar a yau Jumu'a.
 
Daily Nigerian Hausa ta gano cewa duk da PDP ɗin ba ta bada dalilin da ya sanya ta ɗage taron ba, ba ya rasa nasaba da dakatarwar da kotu ta yi wa daya da ga cikin 'yan takarar shugabancin jam'iya na shiyyar, Bello Hayatu Gwarzo sakamakon zargin yi wa jam'iya zangon ƙasa.
Managarciya ta fahimci an samu rabuwar kawuna a tsakanin gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso kan wanda zai zama mataimakin shugaba a Arewa ta Yamma abin da ya hana gudanar da zaben kenan tsawon lokaci.
A satin da ya gabata an ga yanda Tambuwal ya ziyarci jihohi hudu na yankin domin neman goyon baya ga wanda yake son ya yi nasara a zaben, kwatsam sai ga shi kotu a Zariya ta dakatar da wanda ake zaton shi ne Tambuwal ke goyawa baya waton Bello Gwarzo, bayan nan kuma uwar jam'iya ta dakatar da gudanar da zaben sai zuwa wani lokaci kan wasu abubuwa da ba a bayyana ba.