Kiristocin Arewa Ba Za Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba---Mukhtari Shagari

Kiristocin Arewa Ba Za Su Zabi Musulmi Da Musulmi Ba---Mukhtari Shagari

Tsohon  mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Mukhtar Shagari, ya ce jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta yi wa kiristocin arewa laifi, gabanin babban zabe shekarar 2023, Vanguard ta rahoto. 

Shagari ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television da wakilin Legit ya yi nazari.

A cewarsa, APC ta gaza kuma tikitin musulmi da musulmi da ta yi don zaben 2023 ba zai bata sakamakon da ta ke nema ba a arewa. 
"Kiristocin kasar nan, musamman na arewa suna jin a wulakanta su, suna ganin an ci mutuncinsu lokacin da APC ta yanke shawarar yin tikitin musulmi da musulmi." 
Shagari, tsohon ministan albarkatun ruwa kuma mamba na kwamitin amintattu na PDP ya ce idan har dan takarar shugaban kasar na APC, Bola Tinubu, yana da mata kirista, ya kamata ya zabi abokin takara kirista. 
Ya bayyana tikitin na addini guda a matsayin cin mutunci, ya kara da cewa kiristocin Najeriya za su juya wa jam'iyyar mai mulki baya a zaben shugaban kasa da ke tafe.
"Suna tunanin kiristoci da musulmin kasar nan sakarkaru ne. Sun yanke shawarar yin tikitin musulmi da musulmi, suna tunanin hakan zai saka kowa a arewa maso yamma, arewa maso gabas da sauran yan Najeriya za su amince amma yan Najeriya sun waye, sun san abin da suke so; suna son gwamnatin da za ta sauya rayuwarsu."