Kyakkyawan jagorancin Wamakko ne ya sanya mutanen Sakkwato ke goyon bayan APC---Dallatun Wazirin Sokoto
Kyakkyawan jagorancin Wamakko ne ya sanya mutanen Sakkwato ke goyon bayan APC---Dallatun Wazirin Sokoto
Daga Wakiliyarmu
Injiniya Mustapha Mohammad Kofar Marke Dallatun Wazirin Sokoto ya bayyana dalilin da ya sanya jam’iyar APC ke samun tagomashi da daukaka a jihar Sakkwato, har ta zama ba wata jam’iyya a gabanta cikin jihar da yawan mabiya.
Injiniya a zantawasa da manema labarai a wurin gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomin jam'iyar APC a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ya ce kyakkyawan jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ne ya sanya mutanen Sakkwato ke goyon bayan jam'iyar APC domin shi mutum ne da ya san yakamata da yake yi wa jama'a hidima domin cigabansu da farincikinsu.
"Mun gamsu da jagorancin Sanata Wamakko hakan ya sanya APC a Sakkwato take hade tsintsiya madaurinki daya a cikin tsari da bin doka da oda ba wata hatsaniya ko cin zarafin juna." a cewar Dallatun Waziri.
Ya yi kira ga sauran mutanen jiha da ba su cikin jam'iyar APC da su shigo jam'iyar domin ita kadai ce hanya mai kyau ga al'ummar jiha wadda za ta share masu hawaye wurin samar musu da dimbin cigaban da kowa zai yi alfari da su.
Ya ce APC jam'iya ce ta 'yan jiha masu kishin cigaban al'umma da samar da lilwantaccen arziki da kowa zai amfana musamman matasa maza da mata, a kawar da zaman kashe wando da samar da romon dimukuradiyya, domin fahimtar da wnda ake jagoranci mutum ne kamar ka ke jan ragamar tafiyar da harkokin rayuwarka don haka ba zai bari ka shiga halin kunci kan rashin hanya mai kyau da ruwan sha wadatacci da kiyon lafiya ingantacce ko rashin yanayi mai kyau da za ka yi noma, tun a tafiyar farko ya samar maka tsaron rayuwa da dukiyarka.
A karshe ya nemi al'umma su cigaba da marawa APC da jagororinta baya domin samun nasara a zaben 2023 dake tafe.
managarciya