MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Sha Hudu

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Sha Hudu
          _*MEE'AD*_
              
 
*BY*
 
*_HAUWA IBRAHIM MISAU_*
 
%% wattpad__@hauwancyy44 %%
 
  
 
         
 
 
√√√√√ MEE'AD fan's kuyi hakuri da rashin post akan time, sbd wasu dalilai. √√√√√√
 
        
           
                                        31 ~ 32 
 
A firgice take fadin innalillahi wa inna ilaihirrraji'un! Sai a lokacin Majeed ya dubi kan hanya wani mai mashin ya hango ya nufo kansu da gudu da'alama birkinsane ya baci, cikin hanzari da zafin nama Majeed ya sauka a kan titin dakyar yayi parking din moton sai haki yake,"
 
Amal dake zaune a gefensa tuni ta rude sai ihu take kwadawa yayinda Mee'ad ke mai2 kalmar " innalillahi wa inna ilaihirrraji'un," 
 
" A hankali Majeed ya dawo Kai bayan yaji nutsuwa ta sauka masa, zuciyarsa cike da fargaba ya bude moton ya nufi wajen mai mashin din da ya fadi a gefen titi, ya duba jikinsa baiji wani ciyo sosai ba,"
 
Alhamdulillahi Majeed yace kafin ya dubeshi cike da tausayi yace sannu kaji bawan Allah, cike da dauriya mai mashin din yace sannu kayi hakuri kaji, nima kaina banyi tsammanin haka ba, laaah ba komai kakka damu muje na kaika asibiti ko ? 
 
"Jijji kai yayi yana mai nuna alamar bazaije asibiti ba, mutanen dake kewaye dasu ne suke fadin ka tashi ya kaika kaji, laah karku damu banji wani ciyo sosai ba," Majeed yayi iya bakin kokarin sa amma mutumin yaki binsa",
 
Hannu ya sanya bisa aljihun rigarsa ya dauko kudi mai yawa ya mika masa yana fadin Allah ya kara sauki kaji Baba! Karba yayi yana godiya cike da farin ciki.
 
Moto ya dawo ya basu hakuri gamida jin suna lfy ?,  Kafin ya shiga yaja moton cike da nutsuwa.
 
             
                   ✓%%%%%%✓
 
"Karfe 7;30 dai2 suka isa gida bayan yayi parking ya bude kofar moto Amal ta sauka tana murmushi yayinda Mee'ad ta bude kofar moton ta fito hannunta rike da shopping din da sukayi na kayan makulashe,"
 
Majeed ya dubeta kafin yace kawata kawo na rike ledojin hannun naki kinji ? Mika masa tayi tana murmushi.
 
Tare suka jero sun sanyashi a tsakiya fira suke mai dadi sai Daria suke, Majeed cewa yake nikam kun mayar dani kaninku ko? Amal ta kalli fiskarsa gamida kashe ido daya kafin tayi murmushi tace waya isa ya mayar da Yaya kani Kuma? Kallonta yayi cikin ido yana fadin na yarda na zama kani idan har a tare daku ne. 
 
"Murmushi Amal ta karayi ta matso kusa dashi kafin tace koda ka zama kanin Kawarka toni kai Yayanane sbd zuciyata tana kaunarka sosai  Yace da gaske? 
 
"Kafin Amal tayi magana Mee'ad dake tsaye a gefe ta juya baya ta nufi kofar shiga falo fiskarta dauke da murmushin yake yayinda zuciyarta ke mata kuna kamar an zuba tafasashshen ruwa, Majeed ne ya dakatar da ita da cewa Kinga! Ina zakije kuma?"
 
Ba tare data juyo ba ta bashi amsa 'a nitse tana fadin wash! Yaya na gaji sosai ne inaso naje nayi wanka na kwantane, jinjina kai yayi kafin yace alright! good night have a nice dreams my lovely friend! Tnx kawai ta fadi ta nufi cikin gida ba tare data kara cewa komai ba.
 
" Juyowa yayi ya dubi Amal dake tsaye a gefensa kafin yace Farin cikina kema kin gaji ko ? Kije ki kwanta sbd ki tashi da wuri kinga akwai school gobe ko?,
 
"Jijjiga kai tayi kafin tace a'a bangaji ba Yaya ta karasa tana mai shagwabe murya, matsowa kusa da ita yayi gami da riko hannunta shafa gefen fuskarta yayi da dayan hannunsa yana fadin Ina kaunarki fiye da tsammanin ki, inason na kasance dake har karshen rayuwata, pls kimin alkawarin tarayya dani har iya karshen rayuwarki kinji kanwata?,
 
Dago kai tayi ta kalleshi kafin tace nayi maka alkawarin tarayya dakai har karshen rayuwata. 
 
"Murmushi yayi cikin jin dadi kafin yace a iya tinanina nafi kowa farin ciki a dai2 wannan lokacin na gode da 'alkawarin da kikamin kuma insha Allahu zan kula dake dai2 gwargwadona, murmushi tayi kafin ta nufi kofar falo da sauri harta bude kofar sai kuma ta juyo tace My boo kana da kyau! shiyasa nake sonka sosai! Tana fadin haka ta nufi cikin gida da sauri, murmushi yayi kafin ya nufi part dinsa.
 
Mee'ad tana shiga falo bed dinta ta nufa kai tsaye zuciyarta na mata kuna, ji take kamar zata fashe. sunkuyar da kanta tayi bisa gado ta fashe da matsanaicin kuka mai ban tausayi, sai da tayi mai isarta kafin ta tashi jikinta a sanyaye ta nufi toilet.
 
" Yayinda Amal ta shiga bed dinta tana mai farin ciki  har rawa sai da ta taka tana fadin wai nine nake love da hadadden guy kamar Yaya Majeed ? Allah na gode maka.
 
"Dole gobe ya kaini skull dan na goge reni, Dr Majeed kayi kusa zama miji a gareni, juyi take tana daria dauko wayarta tayi ta fara kallon pictures din da suka dauka tana murmushi.
 
" Shima Majeed ya kasance da farin ciki har ya kwanta bacci.
 
*** Washe gari tin karfe 8 Amal ta tashi daga bacci sai a lokacin ta tina da batayi sallan Ishan jiya ba da sauri ta nufi toilet dan yin wanka da alwala.
 
Bata wani jima da fitowa daga wankan ba ta shirya tayi sallolin da 'ake binta bashi, da sauri ta nufi falo danyin break sbd ta shiga skull da wuri. 
 
8;15 ta gama breakfast din tayi waje da sauri sbd 9 asu shiga lecture, 12 kuma za suyi text, kai tsaye motor park ta nufa,"
 
Hangoshi tayi tsaye jikin moto da alamar jiranta yake, sanye yake cikin shigar kananun kaya yayi kyau sosai kamar wani kanuri fuskarta dauke da murmushi ta karasa, gaisheshi tayi kafin tace muje ko ? Bude mata kofar moton yayi kafin ya shiga ciki suka nufi skull dinsu sai fira suke irin tasu ta masoya.
 
Basu wani dau lokaci ba suka isa skull din, sauka Amal tayi a moton ta kira Amrah a waya tana shaida mata cewa ta iso kuma tare da Majeed sukazo. Ihu Amrah ta zuba kafin tace gani nan zuwa.
 
5min da sauke wayar ta hango Amrah  sai sauri take, bata wani dau lokaci ba ta karaso direct kofar moton ta nufa,"
 
"Risinawa tayi cike da kirsa kafin tace Yaya an tashi lfy ? Yaya gajiyar hanya kuma ? Murmushi Majeed yayi kafin ya ce komai Alhmdlh! Ya karatun dai dftn Kunayi sosai, Amrah ta faar da ido kafin tace munayin karatu sosai ma! gud kawai yace, Amrah ta gyara gyalen dake yafe a kafadarta kafin tace Yaya yaushe zakazo gidan mu? Inaso ka rakani unguwa  zare ido Amal tayi cike da bacin rai da mungun kishi tace malama lfy? Mi naji kk cewa ? Gaskiya bazan taba lamuntar irin wadannan furucin ba! Dago kai tayi zuciyarta cike da kuna tajaa dogon numfashi kafin ta budi baki tace.......
 
 
 
Mai karatu biyoni kasha lbr 

What's Your Reaction?

like

dislike

love

funny

angry

sad

wow

News paper