Majalisar Dokokin Zamfara Ta Jefa Kuri’ar Amincewa A Tsige Mataimakin Gwamna
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta jefa uria’r amincewa da tsige Mataimakin Gwamnan Mahdi Aliyu Gusau daga kan muƙaminsa da gagarumin rinjaye, a wani zama a jiya Alhamis da majalisar ta gudanar, ‘yan majalisa 18 cikin 22 ne suka nuna amincewar ɗaukar matakin yayin da ɗaya tak ya ki amincewa, in da yake ganin hakan bai dace ba a yi siyasa ba da gab aba, duk abin da aka soma a kare shi tare ya fi.
‘Yan majalisar sun nemi Alƙalin Alƙalai na Zamfara Mai Shari'a Kulu Aliyu ya kafa kwamatin da zai binciki mataimakin gwamnan bisa zargin saɓa sashe na 190 da 193 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Honorabul Shamsudden Hassan Bosko, shi ne Shugaban Kwamitin yada Labarai na majalisar kuma ya shaida wa Haruna Shehu Tangaza yadda aka yi wannan zaman na amincewa da a salami Mahdi.
Da yawan mutane suna danganta wannan shirin da siyasa wadda ake ganin yakamata gwamnan ya kawar da kansa kanta domin ko ba komai kar ya jawowa kansa fadan da zai yi wahalar samiun nasara kansa.
managarciya