PDP Tanada Tambuwal Babban Daraktan Kamfen Atiku A 2023

PDP Tanada Tambuwal Babban Daraktan Kamfen Atiku A 2023

 

Jam'iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta fitar da jerin sunayen mutane 326 da za su jagorancin yekuwar neman zabenta da ake kira kamfe in da ta nada Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal matsayin Darakta Janar na kamfen din shugaban kasa gaba daya.

A takardar da Sakataren tsare-tsare na jam'iyar a kasa Umar Bature ya sanyawa hannu ta nuna Gwamna Udom Emanuel ne shugaban yakin neman zaben, sai Gwamna Bala Muhammad mataimaki a Arewa, sai Gwamna Seyi Makinde mataimki zai kula da Kudu.
Tsarin mutanen da za su shugabanci tare da jan ragamar yakin neman zaben Atiku bayan Tambuwal DG, Sanata Liyel Imoke da Farfesa Adewale da Raymond Dokpesi da Nwodo a matsayin mataimakansa a bangarori daban daban.
Takardar ta nuna za a kaddamar da kwamitin a ranar Laraba mai zuwa a babban dakin taro na kasa dake Abuja domin fara aiki gadan-gadan.