2023: Dan Takarar Gwamna A PDP Ya Yi Alkawarin Rage Talauci A Yobe

2023: Dan Takarar Gwamna A PDP Ya Yi Alkawarin Rage Talauci A Yobe

 

Daga Muhammad Shamsudeen, Yobe

 

Dan takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam’iyyar PDP Hon. Shariff Abdullahi, ya yi alkawarin bullo da tsare-tsare wajen rage radadin talauci a jihar idan aka zabe shi a 2023.

 
Hon. Sheriff ya yi wannan alkawarin ne a tattaunawarsa da ya yan jaridu, a karshen mako a Damaturu, inda ya ce jihar na bukatar gwamnati mai ingantattun manufofi da tsare-tsare na tattalin arziki wadanda zasu fitar da al'ummar jihar Yobe daga kangin talauci.
 
Bugu da kari kuma ya yi alkawarin kafa cibiyar koyar da sana’o’i da za ta kawar da talauci da tabbatar da inganta tsarin tattalin arziki a kananan hukumomi 17 dake fadin jihar.
 
Ya kara da cewa, "Ina so in tabbatar muku da cewa, zan kafa cibiyoyin koyar da sana'o'i hannu domin samun dogaro da kai a karkashin wani ingantaccen shirin karfafawa da kawar da fatara a jihar Yobe." in ji shi.
 
Ya ce gwamnatin sa a karkashin jam'iyyar PDP ta tsara wani tsari mai inganci domin inganta harkokin noma, ilimi da walwala tare da inganta rayuwar al’ummar jihar.
 
A cewarsa, "Zan aiwatar da manufofi da kudurorin da muke dasu masu ma'ana wadanda suka hada da sake farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa kana da tallafi na musamman ga al'ummar da abin ya shafa da mayar da yan gudun hijira zuwa garuruwansu cikin kankanin lokaci." in ji Shariff.
 
Ya ce daukar matakin farfado da yankunan ya zama dole domin magance matsalolin da wannan rikici na Boko Haram ya haddasa ta hanayar ayyukan jinkai masu ma'ana. Zan kuma gabatar da shirin kula da lafiya da ilimi da bayar da tallafin karatu kyauta a kowane matakin na karatu. 
 
Har wala yau, Dan Takarar PDP ya yi alkawarin warware basussukan da tsoffin ma'aikatan jihar ke bi, wanda ya hada da fensho da kudin sallama, haka kuma da aiwatar da kudurorin gwamnatin sa na kula da jin-dadin ma'aikatan jihar baki daya.
 
Hon. Sheriff Abdullahi ya bukaci al'ummar jihar Yobe su ci gaba da cikakken goyon bayan da suke bashi tare da zabar jam’iyyar PDP da yan takararta a kowane mataki, wanda ta haka ne jihar da Nijeriya za su ci gaba.