Rikicin Shugabanci:Sakataren APC Na Ƙasa Ya Yi Murabus

Rikicin Shugabanci:Sakataren APC Na Ƙasa Ya Yi Murabus

Rikicin Shugabanci:Sakataren APC Na Ƙasa Ya Yi Murabus

Rikicin jam'iya mai mulki ta APC ya ƙara ta'azzara bayan da Sakataren riƙo na jam'iyar na ƙasa, Sanata John James Akpanudoedehe ya ajiye muƙaminsa.

Jaridar The Nation ta jiyo cewa Sakataren ya mika takardar ajiye aikin nasa ne ga sabon shugaban kwamitin riƙo na jam'iyar, Gwamna Abubakar Sani Bello yayin ganawa ta kullum-kullum a Sakateriyar jam'iyar a Abuja.

Rigimar da jam'iyar ke fama da ita ya ɗauki sabon salon a jiya litinin lokacin da aka samu sanarwar dakatar da shugaban jam'iƴar Gwamnan Yobe Mai Mala Buni daga jagoranci, lamarin ya matuƙar ruɗar da mutane a lokacin da ake ciki.