Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe 'Yan Sa-kai 63 A Jihar Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
An gudanar da jana'izar kimanin mutum 63 da suka rasa rayukansu sanadiyar wani harin kwanton ɓauna da 'yan bindiga suka kai wa 'yan Sa-kai a yankin Zuru dake cikin jihar kebbi Arewa maso yammacin Najeriya.
A yammacin ranar Lahadi ne 'yan bindigar suka auka wa yan Sa-kai a kusa da Dirin Daji.
Lamarin ya faru ne a wasu garuruwa na jihar kebbi dake kusa da iyaka da jihar Neja bayan kwanton ɓaunar da yan bindiga suka yi wa yan Sa-kai lokacin da suka rarake su domin ƙwato dukiyar jama'ar da yan bindigar suka yi awon gaba da ita,
Dagacin garin Takita na daga cikin wadanda suka shaida yanda lamarin yake ya kuma ce wa BBC gaskiya sun musu kwanton bauna sun kashe wajen mutum 63.
Lokacin da suka shigo da fari sun kwashi mutane da dabbobi ana ta ihun ga ɓarayi, to bayan sun wuce sai yan Sa-kan suka bi bayansu don ceto wadanda suka kwasa.
To ashe sun yi wa yan Sa-kan kwanton bauna sun buya a saman bishiyoyi, da isar 'yan Sa-kai wajen sai suka bude musu wuta suka kashe su sosai.
Ya ce sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu ne bayan kwaso gawarwakinsu don yin jana'iza
Wadanda aka kashe din sun fito ne daga garuruwa daban-daban ciki har da Takita da sauran wasu garuruwa hudu.
Sai dai ya ce duk da cewa sun samu labarin su ma ɓarayin dajin an kashe wasu daga cikinsu to ba su da tabbas akan yawan wadanda aka kashen.
Lamarin dai ya faru ne ranar Lahadi da misalin karfe 8: zuwa 9: kuma an yi jana'izar tasu da misalin karfe hudu na yamma.
Wani shugaban yan Sa-kai na garin Sanchi, daya daga cikin garuruwan da lamarin ya shafa ya ce sai da suka kirga gawa 63 daga garuruwan Dabai da Magajiya da Takita da kuma Rafin Zuru.
Shi ma kwamadan 'yan Sa-kai na ƙaramar hukumar Zuru ya ce bayan kwaso gawarwakin ne sai suka kai Ofishin 'yan Sanda inda kowane bangare suka je suka kwashi gawarwakin 'yan uwansu.
managarciya