Jarabar Mijina ta Ishe ni Har a Lokacin Al'ada Sai Ya Neme ni---Matar da ta Nemi Kotu ta Raba Aurenta 

Jarabar Mijina ta Ishe ni Har a Lokacin Al'ada Sai Ya Neme ni---Matar da ta Nemi Kotu ta Raba Aurenta 

 

Wata matar aure mai suna Zainab Yunusa ta bukaci kotun shari'a dake zama a Magajin Gari, Kaduna, ta ta tsinke igiyar aurenta da mijinta mai suna Alhaji Ali garba Ali saboda tsabar jarabarsa. Daily Trust ta rahoto, mai karar a ranar laraba ta sanar da kotu cewa Garba na neman jima'i ko a lokutan da take al'adan da lokacin azumin watan Ramadan. 

Zainab tace sun yi zaman aure na shekara daya kacal inda ta kara da cewa ta bar gidansa ne saboda wannan lamarin.
Wacce ke karar ta yi bayanin cewa a yayin zamansu, Garba ya saba dawowa gida har da rana a lokutan da take jinin al'ada don ya kwanta da ita, wanda addinin Islama bai aminta da hakan ba. 
“A yayin azumin watan Ramadan, ya saba dawowa gida da rana kuma ya bukaci kwanciya da ni, idan na ki amincewa sai yayi fushi. "Sannan idan na bukaci abinci, sai yayi martani da cewa in je wurin saurayina ya ciyar da ni. 
“Bai taba yarda da ni ba ta yadda baya barin duk 'yan uwana mata da maza su ziyarce ni"
Matar tace ta bar gidan aurenta saboda bata iya gamsar da mijinta saboda tsabar bukatarsa. 
A don haka ta roko kotun da ta tsinke aurensu saboda bata shirya bin bukatar mijinta ba wurin sabawa Ubangiji. Mijinta, ya musanta ikirarin inda yace Zainab ta shigar da wadannan zargin a kan sa a kotu daban-daban. 
Garba ya sanar da kotun ta bakin lauyansa M.A Sambo cewa, mahaifiyar matarsa ta je har gida sannan ta kwashe kayansa tare da siyarwa daga bisani ta tafi da diyarta. 
Yace mahaifiyarta tayi alkawarin dawo masa da komai da ta dauka a gidan a yayin da suka yi wani zaman sasanci. 
Garba ya bukaci kotun da ta duba bukatarsa na dawo masa da kayansa kafin ya amince da sakin auren.
 Alkali Murtala Nasir bayan sauraron dukkan bangarorin, ya umarci wacce ke karar da ta zo kotu a zama na gaba da mahaifiyarta. 
Ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin cigaba da shari'ar.