Ramadan: kuɗaɗen da Gwamnan Sakkwato ya ware don ciyarwa neman Lada ko La’ada
A kowace shekara watan azumin Ramadan ya kama gwamnoni a Arewa za su rika fitar da makudan kudade da sunan ciyarwa ga mabukata a watan azumin.
Za ka samu gwamna ya ware kudin don a ciyar da mutane abinci a ba su sutura da zimmar a yi ibada cikin kwanciyar hankali Aminiya ta dubi lamarin don fito da hoton da kyau ana yin haka ne don Lada ko don La'ada[abin da za a samu don biyan bukatar duniya].
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin Gwamna Ahmad Aliyu ta ware makudan kudade don ciyarwa azumi in da za ta kashe akalla naira miliyan 998 a ciyarwar.
Gwamnan ne ya sanar da hakan a ranar Talata data gabata a lokacin da yake kaddamar da kwamitin kula da aikin ya ce sun kara yawan wuraren ciyarwa daga 130 zuwa 155.
Gwamnan ya ce akalla mutum dubu 20 ne ake sa ran akullum ya amfana da cibiyoyin a watan azumin Ramadan.
Haka kuma a kalla za a samu mata 610 da wasu 1500 da za su yi aikin wuccin gadi, wannan wata dama ce gare su.
Kafin wannan gwamnati ta raba buhunan masara 990 da dubu 50 ga malamai a masallatan Jumu'a 90 dake birnin Sakkwato, gwamnan ya kuma yi umarni a bayar da tallafi ga wasu sanannun kungiyoyin addini dake jihar.
"Wadan nan kudaden an bayar da su ne da zimmar taimakon malamai da shugabannin addini da suke fadakar da al'umma a wannan watan da bayansa, za mu raba masu kudi ne kamar haka: naira dubu 200 ga manyan malamai 300, dubu 100 malamai 100, dubu 50 ga malaman zaure su 2,900 a dukkan kananan hukumomi 23 na jiha kowace mazaba malami 10.
Sanannen malami a jihar Sakkwato Malam Ishaka Hamis ya yi tsokci kan lamarin ya ce "a janibin addini lamarin nada fuska uku, na farko hakkin Gwamnati ne wajibi da ake bukatar ta sauke ta ga mutane sun samu saukin rayuwa, duk wata hanya za ta bi in ta yi haka tana da lada matukar wannan shi ne makasudin, yana cikin siyasa ta Islama ba kawai sai a watan Ramadan ba, gwamnati samarwa mutane saukin rayuwa.
"A mahanga ta biyu gwamnati za ta dauki nauyin ciyar da marayu da talakawa da ba su iya ciyar da kansu shi ma wannan dole ne ta tabbatar da yunwa ba ta kassara su ba, su samu damar yin ibada in lokacin ya ta'alaka da Ramadan in aka yi haka tana da ladar dauke wajibi da yin shugabanci nagartacce. In ko Gwamnati tana yin ciyawar ne don siyasarsu ta wannan zamani don mutane su kara zabar su ba wata lada akai hasalima suna da zunubi a kai," a cewar Malam Ishaka.
Malam ya kara da cewar "in akwai matsalolin lafiya da ilmi da ruwan sha tau za a yi la'akari ne da kudin ciyarwa da aka yi sun fi karfin lalurar duk abin da ya karu kan haka ya zama laifi, in dai akwai bukatar ciyarwa za a yi sai dai in babu a misali a kwai matsalar lafiya da ilmi da yunwa ka ga gara a fara fitar da mutane yunwa shi ne daidai, matsalar a sanya kudi ne da yawa da yafi bukatar a misali ana bukatar biliyan daya a ciyarwar sai sanya biliyan biyu hakan haramun ne algus ne duk gwamnatin da ta yi haka ba za ta yi nasara ba," in ji Malam.
Wani mai sharhi kan al'amurran yau da kullum a Sakkwato Muhammad Nasir ya soki ciyarwar da gwamnatin ke yi in da yake ganin lamari ne da kawai gwamnati za ta kwashi kudin talakawa wanda hakan bai dace ba.
Ya ce a lissafin da ya yi cibiyoyi 155 da gwamnati ta samar za ta kashe musu miliyan 998, kullum har tsawon kwana 30 kowace cibiya daya za a kashe mata kudi sama da dubu 214, a tsakanin dafa shinkafa da miya da nama da lemu da ruwa da kunu, wannan barnata kudin talakawa ne kawai, wanda ba daidai ba ne.
Yayi kira ga gwamnati ta sanya tsoron Allah acikin zukatansu wanda hakan zai taimake su a mulki tara kudi ba zai kawo masu nasara da cigaban da suke so ba.
Ya ce wannan gwamnati ta dauki malaman addini ne kawai ke bukatar a rika baiwa tallafi akai akai ba tare da kallon matsalolin da mafi rinjayen al'umma ke ciki ba, su kuma masu karatun wannan zamani da ake kira malamai sun yi shiru domin bukatar su na biya, sun mayar da kansu su ne addini da ka yi masu addini ka taimaka, lamarin nan akwai ban takaici sosai a wannan zamani.
managarciya