2027: Za mu dawo mu karbi Sokoto daga 'yan cuwa-cuwa--Abdullahi Hassan ga Gwamnatin Sokoto

2027: Za mu dawo mu karbi Sokoto daga 'yan cuwa-cuwa--Abdullahi Hassan ga Gwamnatin Sokoto

 
 
Dan siyasa jigo a jam'iyar PDP tsohon Kwamishinan muhali da ya taba rike shugaban karamar hukumar Sokoto ta Arewa Honarabul Abdullahi Hassan ya aika sako ga al'ummar jiha da gwamnatin APC karkashin Gwamna Ahmad Aliyu cewa za su yi kokarinsu don ganin mulki ya dawo gefen su.
A wani sako da ya wallafa a turakarsa ta facebook Honarabul ya ce "za mu dawo mu karbi Sokoto daga 'yan cuwa-cuwa da ko na su ba su yi wa adalci, da yardar Allah".
Abdullahi Hassan ya nuna cewa lokacin siyasa ya kama ganin wadanda aka zaba sun shiga cikin shekara ta uku da zabensu da aka yi, don haka za su soma neman hambare wadan da suka samu nasara a 2023 a Sokoto.
Zaben 2027 yana karatowa in da ake ta yin shiri don fara shiga kakar neman kuri'a ga talakawan kasa.